Jam'iyyar APC Ta Ƙasa Ta Ɗauki Mataki Kan Ƴan Takarar Gwamna 12, Bayanai Sun Fito
- Jam'iyyar APC ta tantance ƴan takarar gwamna 12 da zasu fafata a zaben fidda gwani a jihar Edo
- Kwamitin tantance yan takarar jihar Edo ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren tsare-tsaren APC ta ƙasa
- Shugaban kwamitin, Farfesa Taoheed Abdul Adedoja, ya ce dukkan waɗanda suka sayi Fam ɗin takara sun tsallake matakin tantancewa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - All Progressives Congress (APC) ta tantance ƴan takara 12 da ke tseren neman tikitin takarar gwamna a jihar Edo yayin zaben gwamna ke gabatowa.
Kwamitin tantance ƴan takara na jam'iyyar APC ta ƙasa ya gama aikinsa na tantance dukkan masu neman takara gabanin zaben gwamnan Edo mai zuwa a 2024.
Bayan shafe kwana biyu ana aikin tantancewa, shugaban kwamitin mai ƙunshe da mutane 7, Farfesa Taoheed Abdul Adedoja, ya amince dukkan ƴan takarar su fafata a zaben fidda gwani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na kunshe a wata sanarwa da sakataren tsare-tsaren APC na ƙasa, Alhaji Sulaiman Muhammadu Arugungu, ya fitar kuma jam'iyyar ta wallafa a shafinta na X watau Twitter.
Arugungu ya ce duk wadanda aka amince da takararsu za a ba su takardar shaidar tantancewa a ranar Asabar da tsakar rana a sakatariyar jam’iyyar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Kwamitin tantance ‘yan takarar gwamna a jihar Edo ya tantance tare da wanke dukkanin ‘yan takara 12 da suka gabatar da kansu domin tantance su gaban kwamitin."
"Kwamitin ya tantance dukkan ƴan takara 12 da suka sayi fom ɗin nuna sha'awa da tsayawa takara cikin kwana biyu tsakanin Alhamis, 8 ga watan Fabrairu da Jumu'a, 9 ga watan Fabrairu."
Jerin sunayen waɗanda APC ta tantance
1. Prince Clem Agba
2. Sanata Monday Okpebholo
3. HE Lucky Imasuen
4. Honorabul Anamero Sunday Dekeri
5. Fasto Osagie Adrew Ize-Iyamu
6. Injiniya Gideon Ikhine
7. David Imuse
8. Janar Charles Ehigie Airhiavbere (mai ritaya)
9. Farfesa Oserhileimen Osunbor
10. Blessing Agbomhere
11. Honorabul Dennis Idahosa
12. Ernest Afolabi Umakhibe.
Shin Bola Tinubu zai je kallon wasan AFCON na ƙarshe?
A wani rahoton na daban Hukumar CAF ta tabbatar da cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai halarci filin da za a buga wasan ƙarshe a Ivory Coast.
Shugaban CAF, Patrice Motsepe, ya bayyana cewa an faɗa masa Tinubu zai zo kallon wasan ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu, 2024.
Asali: Legit.ng