Akpanudoedehe: Dan Takarar Gwamnan NNPP Ya Lissafa Sharuddan Komawa APC
- Wani dan takarar gwamnan NNPP daga jihar Akwai Ibom ya ce har sai an cika wasu sharudda ne zai iya komawa jam'iyyar APC mai mulki
- Mr John Akpanudoedehe ya ce akwai bukatar ya fara tuntubar magoya bayansa a jam'iyyar NNPP tare da sanin inda jam'iyyar ta dosa
- An gano cewa Akpanudoedehe ya taba rike mukamin sakataren jam'iyyar APC na kasa kafin ya bar jam'iyyar zuwa NNPP a zaben 2023
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Akwa Ibom - Dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a zaben 2023 a jihar Akwa Ibom, John Akpanudoedehe, ya ce labarin karya ake yadawa na cewa ya koma jam’iyyar PDP.
Mista Akpanudoedehe, wanda tsohon sakataren jam’iyyar APC na kasa ne ya bayyana haka a wata hira da Premium Times a ranar Alhamis.
Ya kuma yi watsi da rade-radin cewa zai koma jam’iyyar APC, inda ya ce ba zai iya komawa ba har sai idan an cika wasu sharudda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sharuddan da Akpanudoedehe ya gindaya na komawa APC
Yace:
"Ina so in gaya wa mutane cewa har yanzu ba mu yanke shawarar inda za mu je da abin da za mu yi nan gaba baba. Akwai abubuwa da yawa da ya kamata mu yi a siyasa.
“Sharuddan kafin shiga wata jam’iyya shi ne ka tuntubi magoya bayan ka, sannan jam’iyyar NNPP ta san inda ta dosa da abin da take son cimmawa."
Ya kuma ce ko da shugaban jam’iyyar NNPP na kasa ne ke tunanin komawa jam’iyyar APC, dole ne ya tattauna da magoya bayan jam'iyyar.
Akpanudoedehe, asalin dan PDP ne
Mista Akpanudoedehe, wanda tsohon sanata ne, asalinsa dan jam’iyyar PDP ne, kuma ya taba zama karamin minista na babban birnin tarayya Abuja.
Kimanin shekaru ashirin kenan yana fuskantar adawa a Akwa Ibom bayan ya sauya sheka zuwa jam'iyyar Action Congress of Nigeria, wadda daga baya ta koma APC.
Tsohon sanatan dai ya taba rike mukamin sakataren jam’iyyar APC na kasa, kuma ya tsaya takarar gwamna a 2023 a Akwa Ibom amma Godswill Akpabio ya fi karfinsa.
Rashin gamsuwa da matakin da jam’iyyar ta dauka, Mista Akpanudoedehe ya bar APC zuwa NNPP inda ya samu tikitin tsayawa takarar gwamna, amma ya sha kaye a hannun Umo Eno na PDP.
Shugaban matasan APC ya shirya liyafa don Super Eagles
A ranar Talata Legit Hausa ta ruwaito maku cewa shugaban matasan jam'iyyar APC na kasa, Dayo Israel ya shirya wata liyafar kallon wasan Najeriya da Afrika ta Kudu.
Najeriya ta samu nasara kan Afrika ta Kudu a wasan su na kusa da na karshe wanda ya bata damar zuwa wasan karshe wanda za a yi Lahadi mai zuwa.
Asali: Legit.ng