Hadimin Gwamnan APC Ya Yi murabus Daga amukaminsa a Jihar Arewa, Ya Faɗi Muhimmin Dalili 1

Hadimin Gwamnan APC Ya Yi murabus Daga amukaminsa a Jihar Arewa, Ya Faɗi Muhimmin Dalili 1

  • Mai ba gwamnan jihar Sakkwato shawara ta musamman, Buhari Bello Sahhabi, ya yi murabus daga muƙaminsa ranar 7 ga watan Fabrairu, 2024
  • Tsohon hadimin gwamnan ya miƙa takardar murabus dinsa ga sakataren gwamnatin jihar tare da miƙa godiyarsa ga Allah SWT
  • A cewarsa, wannan mataki ya zama dole saboda yadda a baya-baya aka fara kokarin wulaƙanta shi tare da magoya bayansa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Sokoto - Bayan watanni uku da nada shi a kujerar mai bada shawara ta musamman ga gwamnan jihar Sokoto, Buhari Bello Sahhabi ya yi murabus daga mukamin.

Buhari, wanda aka fi sani da Buhari na Mallam, ya yi murabus daga mukamin ne a wata takarda da ya sanya wa hannu mai dauke da kwanan watan 7 ga watan Fabrairu, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kaduna ya fadi abu guda 1 tak da zai kawo karshen rashin tsaro a Arewa

Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu.
Hadimin Gwamnan Jihar Sakkwato, Buhari Sahabi, Ya Yi Murabus Daga Muƙaminsa Hoto: Ahmad Aliyu
Asali: Facebook

Ya kuma aika wannan takardar zuwa ga sakataren gwamnatin jihar Sakkwato, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa hadimin gwamnan ya yi murabus?

A cikin takardar, tsohon hadimin gwamnan ya ayyana wasu abubuwa da ke faruwa a jihar kwanan nan, waɗanda yake kallo a matsayin sabon salon ci masa fuska.

Ya ce yana ganin waɗannan abubuwa a matsayin wani sabon babi ne da aka buɗe na ci masa fuska tare da magoya bayansa, shiyasa ya aje muƙamin domin tsira da mutunci.

Buhari na Mallam ya ce:

“Cikin tsantsar godiya ga Allah SWT, ni Buhari Bello Sahhabi a wannan rana ta Laraba, 7 ga Fabrairu, 2024, bayan na yi shawarwari da iyalai, abokai, abokan siyasa, da masu fatan alheri nake mika takardar murabus.
"Na miƙa takardar murabus daga matsayin mai ba da shawara na musamman ga Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Gwamnan arewa ya ayyana hutun kwana 1 a jiharsa, ya kawo dalili mai ƙarfi

"Wannan mataki ya zama dole duba da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan na wulakanta ni da magoya bayana da mayar da mu baya.
"Saboda haka, na ɗauki tsattsauran mataki na barin muƙamin da aka naɗa ni a matsayin mai ba da shawara na musamman don tsira da mutunci na."

A halin da ake ciki dai duk wani kokarin jin ta bakin mai magana da yawun gwamna Ahmed Aliyu, Abubakar Bawa, bai yi nasara ba sabida wayarsa ta ƙi shiga.

Gwamna Adeleke zai ɗauki malamai

A wani rahoton kuma Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya amince da ɗaukar sabbin malamai 5,000 da kuma ma'aikatan ilimi 250 a jihar.

Sakataren watsa labaran gwamnan, Olawale Rasheed, ya ce tuni gwamnati ta umarci ma'aikatar ilimi ta fara bin matakan da ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262