Buhari ne sanadi: Jagora a APC ya fadi wanda ya jefa tattalin Najeriya mawuyacin hali

Buhari ne sanadi: Jagora a APC ya fadi wanda ya jefa tattalin Najeriya mawuyacin hali

  • Muaz Magaji ‘Dan sarauniya yana ganin babu wanda ya haifar da matsalar tattali irin Muhammadu Buhari
  • A ra’ayin ‘dan siyasar, ba Shugaba Bola Tinubu ya kashe zomon ba, rataya kurum magabacinsa ya a shi
  • Jagoran tafiyar Win Win ya kawo shawara a tara masana tattalin arziki a tsara yadda za a ceto Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano – Injiniya Muaz Magaji ‘Dan sarauniya fitaccen ‘dan siyasa ne wanda ya shahara musamman a jihar Kano.

A safiyar Litinin, Muaz Magaji ‘Dan sarauniya ya shiga tofa albarkacin baki a Facebook kan halin da Najeriya ta ke.

Buhari
An zargi Muhammadu Buhari da rusa tattali Hoto: Buhari Sallau da Muaz Magaji
Asali: Facebook

Tsohon kwamishinan ayyukan na Kano ya zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da zama silar wuyan da aka shiga.

Kara karanta wannan

Adadin kujerun APC a Majalisa ya bayyana da surukin tsohon Sanata ya zama Sanata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Gaskiyane, Komai na da sanadi!”
“Mu gaya wa kanmu Gaskiya!!”
“Halin da muke ciki!!!”
“Buhari ne Sanadi!”

- Muazu Magaji

Jagoran na Win Win ya ce saboda ganin inda ake neman jefa kasar nan ne suka rika fadakarwa a gwammnatin Buhari.

‘Dan Sarauniya yake cewa watanni takwas da hawan Bola Tinubu, al’umma sun fahimci turbar da aka daura tattalin arziki.

"Buhari ya yi takwas mu na ta jawo hankali a kan irin abin da zai je ya zo in ba ayi hattara ba, kuma in ba muyi hankali ba za muyi barin tafiya!"
"Yau to anzo wajen! SHEKARA TAKWAS fa! Sai ga shi yau a cikin wata takwas kowa ya fahimci inda aka dosa!"

- Muazu Magaji

Ina mafitar matsalar tattali?

A jerin fashin bakin da ya rika yi dandalin zumuntan, tsohon ‘dan takaran gwamnan ya bada shawarar a dage da addu’o’i.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ya barke a Kaduna saboda kashe wanda ya hana sace kuri’un zabe

"Mafita! Mu yi addua Allah ya ba shugabanninmu basirar fitar da mu halin da kasa take ciki…"
"Kuma mu san muhimmancin kuriar mu da dalilin samun mulki a tsarin dimukradyya!"
"Barna sauki gare ta!"
"Gyara ko sai an dage!"
"Balle kuma Barnar Shekaru takwas"

- Muazu Magaji

...A hada da masu kudin Arewa

A cewarsa lokaci ya yi da za a tattaro masana tattali kamar Muhammadu Sanusi II, Shamsuddeen Usman da Mansur Mukhtar.

Burinsa ita ce kwararrun nan su zauna Aliko Dangote, A. A Rano da Abdussamad Rabiu domin su kafa bankunan musulunci.

Daga nan sai ayi amfani da wadannan bankuna da cibiyoyin musulunci wajen kawo cigaba ga tattalin arzikin yankin na Arewa.

Injiniyan ya bada shawara a bada karfi a bangaren noma, albarkatun kasa, makamashi, kasuwanci da kafa kamfanoni.

Tattalin arziki ya yi rauni a yau

Rahoton nan ya nuna yadda ‘yan kasuwa da talakawa su ka komawa ubangiji yayin da farashin kaya su ka haukace a kasuwa.

Kara karanta wannan

Sanata ya fallasa yadda wasu 'Hadimai' suka talauta dukiyar Najeriya a mulkin Buhari kafin 2023

Dalar Amurka ta ki tsayawa a wuri guda, kudin mota kuwa ya dade da tashi sakamakon cire tallafi da Bola Tinubu ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng