Abin da ya sa ba zan ba masu tsaida takara a PDP ko sisi ba - Mai neman Gwamnan Kano
- Injiniya Muazu Magaji ya tabbatar da cewa kudinsa ba za su yi ciwo a zaben tsaida gwani a Kano ba
- ‘Dan Sarauniya ya nuna bai da niyyar batar da kudi saboda samun goyon bayan masu fitar da ‘dan takara
- Muazu Magaji wanda yake takarar Gwamna a PDP ya ce sha’anin shugabanci ya fi karfin a sa a kasuwa
Kano - A lokacin da zaben tsaida ‘yan takarar gwamna ya karaso, Muazu Magaji 'Dan Sarauniya ya ce ba zai kashe kudi wajen samun tikiti ba.
Injiniya Muazu Magaji 'Dan Sarauniya ya yi amfani da shafinsa na Facebook ya na nuna cewa ba zai yi amfani da kudinsa domin samun nasara a zabe ba.
Muazu Magaji Dan Sarauniya wanda shi ne Jagoran Win Win yana cikin masu neman kujerar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP.
Da yake magana a shafinsa, ‘dan siyasar ya ce muhimmancin shugabanci ya fi karfin a saida shi a kan wasu ‘yan kudi, don haka ya yi kira a hada kai da shi.
Shugabanci bai da farashi
“Muhimmancin rikon shugabanci ya fi karfin a saye shi da kudi! Domin kawo karshen abin da ke faruwa yau, sai mu hada kai, mu karbi jihar nan domin cigaban kowa.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Injiniya Muazu Magaji '
Tsohon Kwamishinan ya kara jaddada wannan sako da harshen Hausa bayan yin bayani da Ingilishi.
“Muhimmancin Gwamnati yafi karfin ai mata farashi ko ciniki...zaifi muhada karfi don karbar ragamar Jaharmu don tabbatar da mulkin adalci ga kowa.”
- Injiniya Muazu Magaji
Kafin nan, jigon na PDP ya fadawa Duniya cewa ba zai iya sayen kuri’ar masu fitar da ‘dan takara ba, don haka ya ankarar da su ana yin siyasa ne domin jama’a.
“Ba ZAN IYA sayen kuri’arku domin samun kujera ba. Ina dai bukatar goyon bayanku ne kawai saboda gwamnatin da za mu kafa ta zama ta kowa, ba ta wa ba.”
“Ba zan iya sayen kuri'ar ku ba saboda ina son Jin cewa Gwamnatin da zamuyi ba tawa bace da iyalina, ta Jama'a ce...”
- Injiniya Muazu Magaji
Gwamnatin ci da iyalinka
Injiniya Magaji ya yi alkawari idan ya yi nasarar kafa gwamnati a jihar Kano, al’umma za su amfana, a maimakon ya rika fantamawa da shi da 'yan gidansa.
A baya, Dan Sarauniya ya rika zargin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da cusa iyalinsa cikin gwamnati, har su na damalmala hannu a inda ba su da hurumi.
Masu bibiyarmu su na da labari a ranar Talata, 3 ga watan Mayu, 2022, Salihu Tanko Yakasai ya bada sanarwar zai yi takarar kujerar gwamnan jihar Kano a 2023.
Malam Salihu Yakasai ya shaidawa Duniya wannan ta Facebook. 'Dan siyasar ya taba zama mai bada shawara da kuma Darekta Janar a gidan gwamnatin Kano.
Asali: Legit.ng