Adadin Kujerun APC a Majalisa Ya Bayyana da Surukin Tsohon Sanata Ya Zama Sanata
- Kwamishinan sufuri a Yobe, Musa Mustapha ne zai dare kujerar da Ibrahim Geidam ya bari a Majalisa
- A Ebonyi ta Kudu, Farfesan da APC ta tsaida ya lallasa PDP, APGA da LP a zaben cike gurbin zama Sanata
- Sai nan gaba za a san wanda zai wakilci mutanen Arewacin Filato tun da kotu ta tsige Simon Mwadkwon
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Hukumar INEC ta tabbatar da Musa Mustapha a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan yankin gabashin jihar Yobe.
Daily Nigerian ta ce ‘diyar Musa Mustapha tana auren Ibrahim Geidam wanda shi ya sauka daga kan wannan kujera a 2023.
Tsohon gwamnan ya bar majalisar dattawa ne da Bola Ahmed Tinubu ya nada shi a matsayin Ministan harkokin ‘yan sanda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam’iyyar PDP tana zargin an yi magudi a zaben, wakilinta ya ce APC ta saye kuri’u ne.
APC ta ci Yobe da Ebonyi
The Nation ta ce jam’iyyar APC mai rinjaye a majalisun tarayya ce tayi galaba a zaben Sanata mai wakiltar kudancin Ebonyi.
Farfesa Anthony Ani ya samu kuri’u 46, 270 a zaben da aka shirya, wanda ya zo na biyu shi ne Ifeanyi Eleje (APGA) mai 3, 513.
Silas Onu da jam’iyyarsa ta PDP sun samu 2,783 sai LP da Linus Okorie masu kuri’u 2,710
Sanatoci nawa APC, PDP suke da shi?
Rahoton ya ce yanzu APC tana da Sanatoci 59, sai PDP tana da 37, LP tana da bakwai, jam’iyyun SDP da NNPP suna da biyu.
Jam’iyyar APGA tana da mutum guda a majalisar dattawa, YPP ta rasa kujerarta ga APC.
Idan an yi zaben Sanata Filato ta Arewa za a samu karin kujera. Yanzu an tsaida zaben, an dakatar da jami’in hukumar INEC.
PDP tana nan a kan matsayinta na jam’iyya mara rinjaye a majalisar dattawa da wakilai bayan karin kujerun da APC ta samu.
APC da PDP sun samu kujerun majalisa
Ku na da labari an yi zanga-zanga a jihar Kaduna bayan zaben ‘dan majalisar tarayya na Igabi da aka karasa a karshen makon jiya.
Saboda a sace akwatin zabe, wani ‘dan iskan gari ya dabawa mai shekara 40 wuka a yankin Rigachikun, a sanadiyyar haka ya rasu.
Asali: Legit.ng