Sanata Ya Fallasa Yadda Wasu 'Hadimai' Suka Talauta Dukiyar Najeriya a Mulkin Buhari Kafin 2023
- Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana dalilin da yasa Bola Tinubu ke shan wahala a kokarin saita Najeriya
- Sanata Sani ya jaddada cewa tsohuwar gwamnati ƙarƙashin Muhammadu Buhari ta bar gadon tulin bashi ga gwamnati mai ci
- Jigon PDP ya shaida wa Legit Hausa ranar Laraba, 31 ga watan Janairu cewa Tinubu ya gaji matsaloli da yawa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce hadiman da tsohon shugaban ƙasa, Muhamnadu Buhari, ya kewayen kansa da su sun illata Najeriya.
Sanata Sani ya yi iƙirarin cewa waɗanda Buhari ya aminta ya naɗa a muƙamai sun yi kashe mu raba da dukiyar baitul mali kuma sun gurgunta makomar ƙasar.
Ya bayyana haka ne ranar Laraba, 31 ga watan Janairu, 2023 a wurin tattaunawar da Legit.ng ta shirya 'Twitter Space' mai taken, "Yaƙi da rashawa ko matsalar tsaro: Mafi muhimmanci ga FG a 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma yi iƙirarin cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gaji tulin bashin da ya kai na N77tr daga Buhari, wanda shi ya haifar da matsalar tattalin arzikin da aka shiga.
Abinda ya jawo ƙarin taɓarɓarewar al'amura a Najeriya
Tsohon ɗan majalisar ya ƙara da cewa cin hanci da rashawa da matsalar tsaro na ƙara kamari ne sakamakon rashin iya jagoranci da wawure dukiyar ƙasa a mulkin Buhari.
Sanata Sani ya ce:
“Hanya mafi dacewa wajen yin nazari kan halin da muka wayi gari a ciki ita ce mu tambayi kanmu daga ina muke, me yasa muke nan yau kuma ina muka dosa?
"Mun fito daga wasu shekaru 8, wanda gwamnatin lokacin ta ke ikirarin yaƙi da rashawa amma wasu mutane daga cikinta sun talauta baitul malin ƙasar nan kana sun lalata yau da goben Najeriya.
"Zuwa lokacin da Buhari ya bar gadon mulki, muna da ƴan Najeriya miliyan 113 da ke rayuwa cikin talauci. Sama da mutum 100,000 sun mutu sanadin ƴan ta'adda, rabinsu an yi garkuwa da su.
"Ya tafi ya bar bashin sama da Naira tiriliyan 77 sannan mun ga yadda aka mayar da Babban Bankin Najeriya kasuwa da kuma Uban kirsimeti. Wannan ne fa abin da ya bari a 2023.
“Game da sha'anin tsaro, an kashe tiriliyan Naira karkashin Buhari cikin shekaru 8, ta yadda hatta manyan hafsoshin tsaro na zuwa wurin Buhari da takarda su karbi kudi, wanda shugaban kasa ya amince nan take."
Ministan Tinubu ya maida martani ga dattawan Katsina
A wani rahoton kuma Bello Matawalle ya caccaki dattawan jihar Katsina kan barazanar da suka yi na juya wa Tinubu baya a zaɓen 2027.
Kungiyar dattawan Katsina sun yi barazanar janye goyon bayan Arewa ga Tinubu idan bai sauya tunani kan maida rassan CBN zuwa Legas ba.
Asali: Legit.ng