Babbar Kotu Ta Bada Umarni Kama Shugaban Ma'aikatan Gwamnan PDP da Wasu Mutum 5 Kan Abu 1 Tak

Babbar Kotu Ta Bada Umarni Kama Shugaban Ma'aikatan Gwamnan PDP da Wasu Mutum 5 Kan Abu 1 Tak

  • Kotun tarayya mai zama a Abuja ta bada umarnin damke shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Ribas, Edison Ehie
  • Mai shari'a Emeka Nwite ne ya bada umarnin kama hadimin gwamna Fubara tare da wasu mutane 5 kan kona majalisar dokokin Ribas
  • Rundunar ƴan sanda ce ta shigar da kara gaban kotun kan tsohon kakakin majalisar da kuma sauran waɗanda ake zargi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a birnin tarayya Abuja ta bayar da umarnin kama shugaban ma’aikatan Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas, Edison Ehie.

Kotun ta bada umarnin cafke shugaban ma'aikatan ne kan ƙona wani sashi na zauren majalisar dokokin jihar Ribas, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Duk da suka daga 'yan Arewa ministan Tinubu ya dage kan mayar da FAAN zuwa Legas, ya fadi dalili

Shugaban ma'aikatan gwamnan jihar Ribas, Edison Ehie.
Wata Sabuwa: Babbar Kotu Ta Bada Umarni Kama Shugaban Ma'aikatan Gwamnan PDP Kan Abu 1 Tak Hoto: Edison Ehie
Asali: Facebook

Mai shari'a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja ne ya bada wannan umarnin ranar Laraba, 30 ga watan Janairu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin ya kuma bada umarnin cafkewa tare da gudanar da bincike da gurfanar da wasu mutum 5 da suka haɗa da, Jinjiri Bala, Happy Benedict, Progress Joseph, Adokiye Oyagiri, da Chibuike Peter, wanda aka fi sani da Rambo.

Meyasa kotu ta ɗauki wannan matakin?

Umurnin dai ya biyo bayan bukatar da Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya ya shigar gaban kotu kan tsohon shugaban majalisar dokokin jihar da sauran wadanda ake zargin.

Mataimakin kwamishinan ƴan sanda kuma babban lauya da ya kai matsayin SAN, Simon Lough, ne ya gabatar da bukatar IGP a gaban kotun, Vanguard ta rahoto.

Ya kafa hujja da sashe na 37, 113, 114, 84, da 184 na kundin dokar gudanar da shari’ar manyan laifuka, 2015, da sashi na 35 na kundin tsarin mulkin Najeriya da 32 na Dokar ‘Yan Sanda, 2020.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da gobara ta kama gadan-gadan a wata babbar coci a Najeriya

IGP ya zargi wadanda ake tuhuma da hannu a laifukan da suka hada da hada baki, kone-ƙone, ta’addanci, da kuma kisan wani Sufetan ‘yan sanda, Bako Agbashim da wasu ‘yan sanda 5.

Majalisa ta gayyaci gwamnan CBN

A wani rahoton na daban Majalisar dattawa ta aike da saƙon gayyata ga gwamnan CBN kan muhimman batutuwa da suka shafi tattalin arzikin Najeriya.

Kwamitin kula da harkokin bankuna ne ya faɗi haka jim kaɗan bayan wani zaman gaggawa da ya yi a Abuja ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262