Wata Sabuwa: An Nemi Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Tsige Wasu Ministoci Kan Muhimmin Abu 1
- Wata ƙungiya ta bukaci Bola Ahmed Tinubu ya sa gilashin ba sani ba sabo, ya kori duk ministocin da suka gaza kataɓus
- Ƙungiyar BAVCCA ta kuma ayyana cikakken goyon baya ga gwamnatin Tinubu bisa aiwatar da tsarin dokar man fetur PIA
- Ta kuma bayyana farin ciki da murna tare da jinjinawa shugaban NNPCL bisa gyara matatar man Fatakwal
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ƙungiyar masu fasahar kirkirar shafukan yanar gizo (Bloggers and Vloggers, Content Creators Association in Nigeria) ta aike da saƙo ga Bola Tinubu.
Ƙungiyar wadda ake kira da BAVCCA a taƙaice ta buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya raba gari da dukkan ministocin da suka gaza aikin da aka ɗora musu.
A rahoton Leadership, ta kara da cewa ya zama wajibi shugaban kasa ya kare martabar gwamnatinsa ta hanyar ƙin sassauta wa ragwagen ministoci da marasa gaskiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan kuma kungiyar ta kaɗa kuri'ar goyon bayan Tinubu da shugaban kamfanin mai na kasa, Mele Kyari, kan aiwatar da dokar fetur (PIA) da daidaita ɓangaren mai da gas.
BAVCCA ta bayyana haka ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban kungiyar, Kwamared Ikechukwu Chukwunyere, da sakatare, Alhaji Ibrahim Mohammed.
Ƙungiyar ta yaba da gyaran matatar man Fatakwal
Wani sashin sanarwan ya ce:
"Mun yaba da kokarin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, wajen ɓullo da tsare-tsare da nufin farfado da tattalin arziki, samar da ayyukan yi, inganta ababen more rayuwa, da yaki da cin hanci da rashawa.
"Muna rokon Shugaba Tinubu da ya ba da fifiko kan matakan daidaita farashin canji da kuma karfafa darajar Naira, ta yadda za a samar da ingantaccen yanayin tattalin arziki.
"Muna fatan Shugaban kasa ya gaggauta sauke duk ministocin da suka nuna gazawa domin bai dace a kyale ministoci masu cin hanci da rashawa da malalata ba."
A ƙarshe, ƙungiyar ta taya shugaban ƙasa da Kyari murna bisa samun nasarar sake buɗ matatar man fetur da ke Fatakwal, babban birnin jihar Ribas, rahoton Blueprint.
NLC ta yi magana kan kwamitin mafi ƙarancin albashi
A wani rahoton na daban shugaban NLC na ƙasa ya soki wasu gwamnoni da aka sanya a kwamitin mafi ƙarancin albashi mai ƙunshe da mambobi 37.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya kaddamar da kwamitin ranar Talata a fadar shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng