Jigon Jam’iyyar APC, Danbilki Kwamanda, Zai Cigaba da Zaman Gidan Yari Na Kwanaki
- Alkali Abdulaziz Habib bai je kotunsa na Majistare da ke Kano domin sauraron shari’ar Alhaji Abdulmajid Danbilki
- Rashin halartar alkalin yana da alaka da rashin lafiya da ta ke damunsa, dole kotu ta daga wannan kara sai a Fubrairu
- Kafin a koma gaban alkali, za a cigaba da tsare Abdulmajid Danbilki a gidan gyaran hali bisa zargin tunzura jama’a
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Alkali Abdulaziz Habib bai samu halartar zaman da aka shirya za ayi da Abdulmajid Danbilki a garin kano a ranar Litinin ba.
Daily Nigerian tace rashin halartar Mai shari’a Abdulaziz Habib ya kawo karshen burin Alhaji Abdulmajid Danbilki na samun ‘yanci.
Abdulmajid Danbilki wanda aka fi sani da Danbilki Kwamanda yana tsare saboda zargin tunzara jama’a wajen jawo fitina a Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Laifin da ake tuhumar Danbilki Kwamanda da aikatawa ya ci karo da sashe na 114 na dokar final kwad da ake aiki da ita a jihar Kano.
Mai kare ‘dan siyasar, Ibrahim Abdullahi-Chedi, ya bukaci a bada belinsa a kotun.
Ba za a iya sanin ko Kwamanda ya cancanci beli bisa sashe na 35 (5) da 36 na kundin tsarin mulki ba saboda rashin lafiyar alkalin.
Babban alkalin kotun na majistare da ke zama a garin Kano bai da lafiya, saboda haka ba a saurari karar da aka yi niyya yau ba.
Rahoto yace an daga shari’ar zuwa ranar 1 ga watan Fubrairu saboda rashin lafiyar.
Magatakardan kotun ya sanar da cewa Abdulaziz Habib bai jin dadi don haka bai zo aiki ba, abin da ya jawo mai shari’a ya tafi asibiti.
Abdussalam Saleh yana zargin ‘dan adawan da kira ga jama’a su shirya fito na fito da gwamnatin Kano a kan yunkurin taba masarautu.
'Dan adawan na NNPP ya dauki hayar Barista Ibrahim-Chedi ya karyata zargin da ake yi masa, tuni aka tsare shi a gidan gyaran hali.
Lauyan ya zanta da gidan rediyon Premier, ya tabbatar da wannan zance a dazu.
Bayan Danbilki saura Kibiya
Bayan kama Ɗanbilki Kwamanda, an ji labari 'yan adawa suna so tsohon kwamishinan Kano ya bi sahunsa a gidan gyaran hali.
Salihu Tanko Yakasai wanda aka fi sani da Ɗawisu ya bukaci a cafke Adamu Kibiya saboda yi wa alkalan kotun korafin zabe barazana.
Asali: Legit.ng