Kalaman Buhari Sun Jawo Za a Binciki Inda Gwamnoni 150 da Ministoci Suka Kai N40tr
- SERAP tana son sanin gaskiyar kudin da aka ba kananan hukumomi tun da aka dawo mulkin farar hula
- Daga shekarar 1999 har zuwa yanzu, kungiyar tana ikirarin an raba N40tr ga kananan hukumomi
- Tsoron da ake yi shi ne mafi yawan wadannan kudi sun kare ne a aljihun jami’an gwamnatin jiha
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Kungiyar SERAP ta bukaci gwamnonin jihohi 36 da ke kasar nan su fadi adadin kudin da ake warewa kananan hukumomi.
Rahoton Channels yace kungiyar ta nemi gwamnoni da ministan Abuja suyi bayanin kason kananan hukumomi tun daga 1999 zuwa yau.
Muhammadu Buhari ya hada gwamnoni da aiki
A wani bidiyo da yake yawo, an ji Muhammadu Buhari yana bayanin yadda gwamnoni suke rub-da-ciki kan kudin talakawansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin shugaban SERAP na kasa, Kolawole Oluwadare, ya rubuta takarda a ranar Asabar da nufin samun wadannan bayanai.
Kolawole Oluwadare yace al’umma suna da damar sanin yadda aka yi kason kudi a asusun FAACC, aka rabawa kowane matakin gwamnati.
Kamar yadda labari ya zo daga shafin kungiyar a X, ana so jihohi da Abuja su rika sannu-sannu da dukiyar jama’an da ta biyo hannunsu.
Takardar SERAP tana so nan da kwanaki bakwai a samu amsar tambayarsu, muddin hakan bai samu ba, kungiyar za ta kai kara a kotu.
Shugaban kungiyar yake cewa kishin al’umma ta sa suka nemi wadannan bayanai. Ba wannan ne karon farko da ta taso hukuma a gaba ba.
Idan aka yi gaskiya wajen batar da dukiyar kananan hukumomi, za a magance satar da ake yi a baitul-mali, ayi wa talaka aikin da zai more.
Abin da kungiyar take zargi shi ne, a sakamakon taba dukiyar kananan hukumomi ake fama da masifar talauci, rashin cigaba da aiki.
EFCC da ICPC su binciki N40tr
Oluwadare yace gwamnoni da ministan Abuja sun karbi N40tr da sunanan kananan hukumomi, daga ciki akwai N483bn a karshen bara.
Wannan kungiya ta kuma nemi gwamnonin jihohi da ministan harkokin Abuja su gayyaci ICPC ds EFCC domin su gudanar da bincike.
Kwankwasiyya-Ganduje
Hadakar APC da NNPP za ta iya sanadiyyar aika PDP makabartar siyasa a Kano da dinkewar'yan Kwankwasiyya da mutanenGandujiyya.
Makomar Abba Gida Gida da Nasiru Gawuna tana neman canzawa makonni 2 da yin hukuncin zaben gwamnan jihar Kano a kotun koli.
Asali: Legit.ng