Kano: Bayan Ganduje, Shugaban Gwamnonin APC Ya Tura Muhimmin Sako Ga Abba Kabir Kan Komawa Jam’iyyar
- Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya bayyana amfanin jihar Kano a siyasar Najeriya bai daya
- Uzodinma wanda shi ne shugaban gwamnonin APC ya bayyana haka a jiya Alhamis 25 ga watan Janairu
- Wannan na zuwa ne bayan Ganduje ya roki Abba Kabir ya shigo jam’iyyar don inganta siyasar jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Shugaban gwamnonin APC a Najeriya, Hope Uzodinma ya tura roko ga Gwamna Abba Kabir na Kano kan komawa APC.
Uzodinma ya yi wannan roko ne yayin da shugaban APC, Dakta Abdullahi Ganduje ya roki gwamnan don komawa APC.
Sakon Ganduje ga Abba Kabir
A jiya Alhamis ce 25 ga watan Janairu Ganduje ya roki gwamnan da ya shigo jam’iyyar don inganta siyasar jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganduje ya ce komawar Abba APC zai kara inganta siyasar jihar da kuma ci gaban al’ummar jihar, cewar Daily Nigerian.
Ya ce jam’iyyar na iya kokarinta don ganin ta damko sauran ‘yan Majalisun Tarayya da ke jihar.
A bangarenshi, Gwamna Uzodinma na jihar Imo ya bayyana haka a jiya Alhamis 25 ga watan Janairua fadar shugaban kasa.
Martanin Uzodinma ga Abba Kabir
Uzodinma ya ce Kano ta na da matukar muhimmanci ba iya jihar ba duk Najeriya baki daya a siyasance, cewar Punch.
A cewarsa:
“Kano ba iya jihar take da muhimmanci ba a Najeriya baki daya ta na da matukat tasiri, don haka ta na da muhimmanci a gare mu.
“NNPP jam’iyya ce haka APC ita ma jam’iyya ce, babban abu mai muhimmanci shi ne kare muradun ‘yan Najeriya.”
Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya yi zama na musamman da masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC a jihar Kano.
Tawagar ta samu jagorancin Dakta Umar Ganduje inda ya samu rakiyar dan takarar jam’iyyar a jihar Nasiru Gawuna, cewar Independent.
Ganduje ya roki Abba Kabir
Kun ji cewa shugaban jam’iyyar APC a Najeriya, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya roki Gwamna Abba Kabir ya dawo APC.
Ganduje ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 25 ga watan Janairu inda ya ce hakan zai kara inganta siyasar jihar.
Asali: Legit.ng