NNPP Vs Kefas: Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar Gwamnan Jihar Taraba
- A ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu, Kotun Ƙoli ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Taraba da aka gudanar a watan Maris, 2023
- Kotun ta tabbatar da cewa Agbu Kefas ne halastacce kuma zaɓaɓɓen gwamnan jihar, tare da yin watsi da korafin NNPP
- Tun da fari, Farfesa Yahaya Sani, dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar NNPP ya shigar da karar yana neman a tsige Kefas
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Rahotannin da muka samu na nuni da cewa Kotun Koli ta tabbatar da Agbu Kefas matsayin zababben gwamnan jihar Taraba.
Kotun Kolin ta yi watsi da karar da Farfesa Yahaya Sani na jam'iyyar NNPP ya shigar saboda karancin kwararan hujjoji, Channels TV ta ruwaito.
Kotun Koli ta yi watsi da korafe-korafen NNPP
Farfesa Sani ya bukaci Kotun Kolin da ta yi watsi da nasarar da gwamna Kefas Agbu ya samu a zaben gwamna da aka yi ranar 18 ga Maris, 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi zargin rashin bin dokar zabe, rashin bin ka’ida da sauran munanan ayyuka da aka tafka a yayin zaben.
Ya bukaci kotun da ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben bisa dalilin samun rinjayen kuri'un da aka kada.
Abin da ya faru a Kotun Daukaka Kara da Kotun zaben Taraba
Kotun daukaka kara da ke Abuja a watan Nuwamba ta yi watsi da karar da Sani ya daukaka kan hukuncin da kotun kararrakin zabe ta yanke na tabbatar da zaben Kefas.
A hukuncin da ta yanke, ta yi watsi da karar da jam’iyyar NNPP ta shigar saboda rashin cancanta kamar yadda karamar kotun ta yi a ranar 30 ga watan Satumba.
Gwamna Kefas ya samu kuri’u 257,926 inda ya kayar da Yahaya wanda ya samu kuri’u 202,277 a zaben gwamnan da aka yi a ranar 18 ga Maris, 2023.
Sokoto: Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Ahmad Aliyu
A wani labarin makamancin wannan, Kotun Koli ta tabbatar da cewa Gwamna Ahmad Aliyu ne wanda ya lashe zaben jihar Sokoto da aka gudanar a watan Maris, 2023.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyar PDP da tan takararta Sa'idu Umar suka shigar na neman a tsige Aliyu daga kujerar gwamnan.
Asali: Legit.ng