Gaskiyar ta fito: Abu 1 da Ya Sa Aka Tsige Shugaban Majalisar Dokokin Jihar APC Daga Muƙaminsa

Gaskiyar ta fito: Abu 1 da Ya Sa Aka Tsige Shugaban Majalisar Dokokin Jihar APC Daga Muƙaminsa

  • Ɗan majalisa ya bayyana asalin dalilin da ya sa aka tsige shugaban majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo
  • Ranar Talata, 22 ga watan Janairu, ƴan majalisa 18 cikin 26 suka tsige kakakin majalisar bisa zargin almubazzaranci da kuɗinsu
  • Da yake jawabi ga ƴan jarida, Soneye Kayode ya ce dama tun usuli ba su so zabensa ba amma APC ta matsa lamba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Mamba mai wakiltar mazaɓar Obafemi Owode a majalisar dokokin jihar Ogun, Soneye Kayode, ya bayyana maƙasudin tsige kakakin majalisar, Olakunle Oluomo.

A ranar Talata, ƴan majalisa 18 daga cikin 26 suka tsige kakakin majalisar dokokin jihar Ogun daga kan kujerarsa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Majalisa ta ɗauki mataki 1 awanni kaɗan bayan gwamnan APC ya naɗa sabon mataimakin gwamna

Tsohon kakakin majalisar Ogun.
Gaskiyar Dalilin da Ya Sa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ogun Ya Rasa Kujerarsa Hoto: Olakunle Oluomo
Asali: UGC

Daga bisani kuma mambobin suka zabi Honorabul Oludaisi Elemide a matsayin sabon kakakin majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa ƴan majalisar sun tuge Oluomo ne bisa zargin da suke masa na almubazzaranci da kudade.

Gaskiyar dalilin tsige shugaban majalisar Ogun

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaman majalisar, Kayode ya ce mambobin majalisar ba su so zaben Oluomo a matsayin kakakin majalisar ba tun farko.

Amma a cewarsa shugabancin jam'iyyar APC mai mulki ya fi aminta da shi ya jagoranci majalisar saboda gogewar da yake da ita.

Dan majalisar ya zargi Mista Oluomo da yin sharholiya da kudaden da aka tanadar wa ‘yan majalisar jihar Ogun.

A kalamansa ya ce:

"Abinda ya afku shi ne Oluomo yana yawonsa ya je duk inda yake so, amma sai ya zo wajen mu ƴan majalisa ya faɗa mana har yanzu gwamna bai turo mana kuɗi ɓa, mu ci gaba da maneji.

Kara karanta wannan

Filato: Ƴan majalisa 16 na arewa da suka samu nasara a kotun ɗaukaka kara sun shiga matsala

"Haka muka ci gaba da hakuri, daga bisani muka gano ashe gwamna ya sa hannu an turo mana kudi. Ya rubuta takarda ya kaima gwamna kuma ya ba shi kuɗi amma ya cinye."

Shin Gwamna Abiodun na da hannu a lamarin?

Kayode ya ce tsige Oluomo ba shi da alaka da Dapo Abiodun, gwamnan jihar, inda ya ce gwamnan baya tsoma baki a harkokin majalisar.

Dan majalisar ya bukaci Oluomo ya mayar da hankali kan shari’ar da ke gabansa kan zargin da ake masa na halasta kudim haram, Leadership ta ruwaito.

A watan Satumban 2022, hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta kama Oluomo bisa zargin almundahana da kudi.

PDP ta ƙara shiga matsalar shari'a

A wani rahoton kuma Abubuwa na neman ƙara dagulewa jam'iyyar PDP kan rashin shirya taron kwamitin zartarwa (NEC) na ƙasa.

Ɗan takarar gwamna a jihar Ogun a zaben 2023, Sowunmi, ya maka shugabannin PDP a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262