Ana Cikin Rade-Radin Dawowar Kwankwaso APC, Ganduje Ya Sha Sabon Alwashi Kan Abu 1
- Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashi kan zaɓukan cike gurbi da za a yi
- Ganduje ya sha wannan sabon alwashin a wajen yaƙin neman zaɓen ɗan takarar sanatan jam'iyyar na mazaɓar Yobe ta Gabas
- Shugaban na APC ya kuma bayyana cewa jam'iyyar a shirye take ta bayar da dukkan goyon bayan da ya dace domin ya samu nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Yobe - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bada tabbacin cewa jam’iyyar za ta lashe dukkan zaɓukan cike gurbi da za a yi.
Ganduje ya bayyana hakan ne a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, wajen yaƙin neman zaɓen ɗan takarar sanatan jam'iyyar na Yobe ta Gabas a zaɓen da za a yi ranar 3 ga watan Fabrairun 2023, cewar rahoton The Nation.
Jaridar Blueprint ta ce a tare da Ganduje akwai shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma taron gangamin yaƙin neman zaɓen ya samu halartar mai masaukin baƙi Gwamna Mai Mala Buni, ministan harkokin ƴan sanda Sanata Ibrahim Gaidam da tsohon shugaban majalisar dattawa ta tara Dakta Ahmed Lawan.
Wane tabbaci Ganduje ya ba da?
Ganduje ya ba da tabbacin cewa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC na ƙasa, zai bayar da cikakken goyon bayansa don ganin nasarar ɗan takararta a Yobe, Musa Mustapha wanda aka fi sani da Coolas da sauran ƴan takara a zaɓukan cike gurbin.
A cikin kwanakinnan ne dai aka zaɓi Musa Mustapha a matsayin ɗan takarar sanatan jam'iyyar na Yobe ta Gabas.
Idan ya yi nasara, zai maye gurbin surukinsa Sanata Ibrahim Geidam, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa muƙamin minista.
Ganduje Ya Magantu Kan Nasarar APC a Imo da Kogi
A baya rahoto ya zo cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya fayyace dalilin da ya sa jam'iyyar ta lashe zaɓukan gwamnonin jihohin Kogi da Imo.
Ganduje ya bayyana cewa APC ta samu wannan nasarar ne saboda gamsuwa da salon mulkinta da ƴan Najeriya suka yi.
Asali: Legit.ng