Shugaban Kasa Tinubu Ya Dage Zai Daurawa Jam'iyyar APC da NNPP Auren Dole a Kano
- Ana zargin Bola Ahmed Tinubu ya dage a kan maganar yin sulhu da ‘yan jam’iyyar NNPP a Kano
- Jiga-jigan jam’iyyar APC sun ji lamarin ya yi masu bam-barakwai, amma da alamar babu yadda za suyi
- Ganduje ya shiga tsaka mai wuya tsakanin sasantawa da Rabiu Kwankwaso da makomar kujerarsa a APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya fara kokarin ganin ya dawo da Rabiu Musa Kwankwaso jam’iyyar APC da ya bari a 2018.
Wani rahoto da aka samu daga Daily Trust ya tabbatar da Shugaban kasar ya bukaci Abdullahi Umar Ganduje ya jawo ‘yan NNPP.
A zaman da ya yi da jagororin jam’iyyar APC mai mulki na reshen Kano, Bola Tinubu ya nuna bukatar a shigo da Rabiu Kwankwaso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sulhun APC v NNPP: Ganduje zai shigo Kano
Majiyarmu ta shaida cewa shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje zai zauna da ‘ya ‘yan jam’iyya a Kano domin a fara maganar.
Sai dai wasu daga cikin magoya bayan APC da tsohon gwamnan na Kano sun nuna rashin gamsuwa da wannan yunkuri da ake yi.
Jaridar tace da shugaban kasa ya zauna da manyan APC na jihar Kano ne ya bijiro da wannan shawara, kuma babu wanda ya ja da shi.
Shawarar sasantawa ko umarni ga APC?
Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa shawara ce kurum mai girma shugaban kasa ya bada, ba umarnin hada-kai da ‘yan adawa ba.
‘Dan majalisar ya ce hakan ba laifi ba ne muddin za ayi sulhun ne da kyakkyawar manufa.
Tinubu ya hadu da Kwankwaso
Idan labarin ya tabbata, shugaba Bola Tinubu ya zauna da jagoran NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso a kan batun a makon da ya wuce.
Ana tunanin shugaban Najeriyan ya yi wa Kwankwaso bayanin bukatar dawowarsa APC da suka yi wani zama na sirri a fadar Aso Villa.
Auren dole za ayi wa APC da NNPP?
Wasu daga cikin magoya bayan Kwankwasiyya sun fara nuna dar-dar game da sasanta su da ake neman yi da ‘yan Gandujiyya da APC.
A gefe guda, Legit ta lura akwai masu ganin hakan ba laifi idan za a dama da Kwankwaso ko a karshe za ayi watsi da Abdullahi Ganduje.
Kwankwaso yana nan a NNPP
Amma a wata hira da muka yi da Buba Galadima, yace mana babu wani alkawarin da aka yi da Rabiu Musa Kwankwaso a kan sauya-sheka.
Galadima yayi zancen siyasar Kano da takarar madugun darikar Kwankwasiyya a zaben 2027, ya ce zuwa yanzu ba a sasanta da APC ba.
Asali: Legit.ng