Kayode Fayemi ya yi watsi da hotunansa na takarar Shugaban kasa da ke yawo a Gari

Kayode Fayemi ya yi watsi da hotunansa na takarar Shugaban kasa da ke yawo a Gari

- Hotunan neman takarar Gwamna Kayode Fayemi sun fara ratsa gari tun yanzu

- Gwamnan Ekiti ya ce babu abin da ya hada shi da wadannan fastoci da ake gani

- Fayemi ya gargadi masu wannan aiki su guji karambani, su tsaya a hurumin su

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya nuna babu abin da ya hada shi da hotunansa da ake gani su na zagaye gari da nufin zai tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

Dr. Kayode Fayemi ya ce babu ruwansa da wadannan fostoci da wani shugaban karamar hukuma na jihar Ekiti ya fito da su a kafafen yada labarai da sadarwa na zamani.

Mai girma gwamnan ya ce Femi Ayodele bai da hurumin da zai fito da fosta da sunan zai yi takara a zaben 2023. Ayodele shi ne shugaban karamar hukumar Ikere a Ekiti.

Da ya ke magana game da wadannan hotuna na takarar 2023, ta bakin babban sakataren yada labarai na gwamnatin jihar Ekiti, gwamnan ya ja-kunnen masu wannan aiki.

KU KARANTA: Oshiomhole sun kitsa yadda za a yi mana dauki dai-daya a zaben Edo - PDP

A jiya jaridar Vanguard ta rahoto Mista Yinka Oyebode ya na cewa: “Dr. Kayode (Fayemi) bai san labarin hotunan yakin neman zabensa ba, kuma bai bada umarnin ayi ba.”

Yinka Oyebode ya kara da cewa Femi (Ayodele) ko wani mutum ko kungiya bai da hurumin da zai yi magana a madadin gwamnan ta fuskar mulki, siyasa, da shugabanci.

“Gwamna Fayemi ya fada, ya nanata sau da-dama cewa ya na da wa’adin shekaru hudu ne a matsayinsa na gwamnan jihar Ekiti kuma burinsa shi ne cika alkawuran da ya dauka.”

Sakataren yada labaran ya ke cewa gwamnatin mai girma Fayemi za ta cin ma nufinta ne ta tsarin ingantaccen shugabanci da dabbaka manufofin da ya kawo na kawo cigaba.

Fayemi ya gargadi jami’an gwamnatin Ekiti ‘ka da su kauracewa siyasa mai tsabta, tare da gujewa abubuwan da za su karkatar da akalar gwamnati, jam’iyyar da gwamna.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng