Buhari bai damu da daukan hotuna ba, inji mai hoton shi na musamman

Buhari bai damu da daukan hotuna ba, inji mai hoton shi na musamman

-Bayo Omoboriowo ya wallafa littafi game da Shugaba Buhari a karo na biyu

-Matashin wanda shi ne mai daukan hoton na musamman na shugaban kasa ya ce Buhari ba mutum bane dake gyara domin kawai yana so dauke shi hoto

Bayo Omoboriowo wanda shi ne mai daukan Shugaba Buhari hoto na musamman ya bayyana cikin wani litttafin da ya wallafa mai shafi 314, cewa hotunan Buhari na nuna yadda yake ne a zahiri.

Bayo ya sake rubuta wani littafin da Buhari ya wallafa kwanan nan shi kuma mai shafi 330 mai taken "Zama Buhari” inda ya bayyana cewa shugaban ba mutum bane wanda ke daidaituwa domin kawai a dauke shi hoto.

KU KARANTA:Tsohon gwamnan Zamfara yayi watsi da rahoton da aka rubutawa APC a kan shi

Har wa yau, marubucin wadannan littatafai ya zanta da masu kula da labarai na fadar shugaban kasa a ranar Laraba 19 ga watan Yunin 2019, ga kuma yadda tattaunawar ta su ta kasance:

Kwanan nan ka rubuta sabon littafi mai taken ‘Zama Buhari’ wanda shugaban kasa ya kaddamar a ranar Talata, ko me ya janyo ka rubuta wannan littafi?

Bayo: A farko dai wannan littafin da na rubuta cigaban na farko ne wanda na rubuta a shekarar 2016, wanda na sanya wa taken ‘Buhari: Damina uwar albarka’. Abinda ya sa ni na rubuta wannan littafi na biyu shi ne domin in bar wa diya na tarihi da kuma labarin wane ne Buhari kamar yadda nima na taso a gida na samu littafan Wole Soyinka, Obafemi Awolowo da Nnamdi Azikwe.

Me kake kokarin sanar da ‘yan Najeriya da har ka sanya wa littafin taken ‘Zama Buhari’?

Daya daga cikin abubuwan da nake a kan hotunan Shugaba Buhari shi ne nuna ma jama’a hakikanin waye Buhari. Duk wani hoton da zaku gani cikin littafin yana nuna muku ainihin wane ne shugaban kasa ne a zahiri.

Akwai abubuwan da suka wakana tsakanin 2015 zuwa 2019 a cikin littafinka kuwa?

Tabbas akwai, nayi magana kan yaki da cin hanci, kokarin samar da tsaro da kuma zaman lafiya da shugaban kasar keyi, tun daga inda ya fara da kuma inda ake a yanzu.

Wane sako kake kokarin isar wa jama’a cikin littafin naka?

Duk da cewa dai mutane na gani hotuna ne kawai a shafukan sada zumunta zamani wadanda ba’a dauke su da muhimmanci ba, ko shakka babu hotunan shugaban haqiqaninsa suke nuna wa. A kullum tunaninsa bai wuce na cigaban Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel