Shugaba Tinubu Ya Taya Jigon PDP Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa, Ya Fadi Kyakkyawan Halinsa

Shugaba Tinubu Ya Taya Jigon PDP Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa, Ya Fadi Kyakkyawan Halinsa

  • Shugaba Bola Tinubu ya taya Reno Omokri, tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, murnar zagayowar ranar haihuwarsa
  • Tinubu ya taya fitaccen mai sharhin kan al'amura kuma ɗan siyasa murna tare da yaba masa bisa yadda ya taka rawar gani wajen bayar da ra’ayoyi masu ma’ana kan al’amuran ƙasa
  • Omokri ya mayar da martani ga sakon taya murnar na shugaban ƙasan ta shafinsa na X a ranar Litinin, 22 ga watan Janairu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya fitaccen ɗan jam’iyyar PDP, Reno Omokri murnar cika shekara 50 da haihuwa a duniya.

Omokri dai na murnar zagayowar ranar haihuwarsa a ranar Litinin, 22 ga watan Janairu, 2024. Ya cika shekaru 50 a duniya.

Kara karanta wannan

Buhari ya faɗi dalilin da ya sa gwamnatinsa ba ta kashe wani shugaban ƴan ta'adda ba, ta yi masa gata 1

Tinubu ya taya Omokri murna cika shekara 50
Shugaba Tinubu ya taya Omokri murnar cika shekara 50 a duniya Hoto: Reno Omokri, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu ya jinjinawa Omokri

A wata sanarwa da Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban ƙasar ya sanya wa hannu, Shugaba Tinubu ya yabawa Omokri bisa yadda ya taka rawar gani wajen bayar da ra'ayoyi masu ma'ana kan al'amuran ƙasa, ba tare da la'akari da siyasa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Reno Omokri ya kasance mataimaki na musamman kan kafafen sadarwa na zamani ga tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan daga shekarar 2011 zuwa 2015.

Shugaba Tinubu, jigo a jam'iyyar APC mai mulki, ya yi wa Omokri fatan samun ƙarin shekaru masu yawa a cikin ƙoshin lafiya "yayin da shi (Omokri) ke ci gaba da ba da gudummawarsa ga ci gaban ƙasa".

Reno Omokri ya yi martani

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na sada zumunta, Omokri ya nuna godiya ga Allah da ya bar shi a raye. Ya kuma godewa Shugaba Tinubu bisa yabon da ya yi masa.

Kara karanta wannan

Bayan nasara a Kotun Koli, gwamnan APC ya bayyana makomar siyasarsa bayan gama mulki

A kalamansa:

"A yau ina da shekaru 50, kuma ina godiya ga Allah da ya ba ni ni’imar rayuwa mai tsawo. Ina girmama iyayena da suka rasu, mai shari'a Omokri da Otolu (ma’ana Gimbiya) Bemigho.
"Godiya ta musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yaba min tare da taya ni murna a wannan rana."

Omokri Ya Kwatanta Mulkin Tinubu da Na Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa Reno Omokri ya yi magana kan salon mulkin Shugaba Tinubu da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Jigon na jam'iyyar PDP ya lissafo dalilai tara waɗanda suka sanya mulkin Shugaba Tinubu ya fi na Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng