Yadda Muka Taimaki APC Aka Haifar da Gwamnatin Buhari a 2015, Tsohon Gwamnan PDP

Yadda Muka Taimaki APC Aka Haifar da Gwamnatin Buhari a 2015, Tsohon Gwamnan PDP

  • Sule Lamido ya maidawa Bisi Akande martani da ya ce za a sha wahala muddin PDP ta dawo mulki
  • Tsohon gwamnan Jigawa yake cewa yanzu al’ummar Najeriya ba dadi suke ji a gwamnatin APC
  • Sule ya tunawa Akande yadda aka kafa jam’iyyarsu ta APC da taimakon gwamnoni da kusoshin PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Jigawa - Sule Lamido ya yi wa Bisi Akande raddi bayan wasu kalamai da ya yi na cewa za a shiga wahala idan PDP ta koma mulki.

Tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya zanta da BBC Hausa bayan maganganun da tsohon shugaban rikon kwaryan jam’iyyar APC ya yi.

APC v PDP
APC v PDP: Sule Lamido da Bisi Akande Hoto: bisiakande.com
Asali: UGC

Alhaji Sule Lamido ya aikawa dattijon martani ne ganin cewa da su aka kafa PDP kuma a karkashin jam’iyyar ya samu mulki a 2015.

Kara karanta wannan

Farfesa Soyinka zai fito da sunayen ‘yan APC da ya kamata EFCC, ICPC su cafke

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sule Lamido ya ce tsufa yake damun Akande

Tsohon gwamnan ya ba Bisi Akande uzuri duk da sukar da ya yi wa jam’iyyarsa, dalilinsa kuwa shi ne ganin ya kai shekaru 85.

Sule ya tunawa Akande a zabukan da aka yi a 1999 da 2003 da 2007 da 2011, kuri'un PDP ya sha gaban na ragowar sauran jam’iyyu.

'Yan PDP suka kafa APC a mulki

‘Dan siyasar ya ce APC da ‘yan adawa ba su iya karbe mulki daga hannunsu ba sai lokacin da aka samu goyon baya daga manyan PDP.

A zaben 2015, Sule ya ce Olusegun Obasanjo, Bukola Saraki, Atiku, Abdullahi Adamu da irinsu Aminu Tambuwal suka taimaki APC.

Jagororin jam’iyyar PDP da gwamnonin jihohi irinsu Rabiu Kwankwaso, suka sauya-sheka zuwa APC har aka kifar da gwamnatin Jonathan.

Saboda haka tsohon ministan harkokin wajen ya kira mulkin Muhammadu Buhari da haramtaciyyar gwamnatin ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

An shiga uku a PDP, mutumin Atiku yana barazanar kai shugabannin jam’iyya kotu

Ko da ana yi wa mugun kallo a yau, Sule ya fadawa Akande cewa hada-kai da aka yi da jiga-jigansu ne ya haifar da mulkin APC a Najeriya.

An fi wahala a lokacin APC ko PDP?

Jigon na PDP ya kara da fadawa BBC zuwan APC bai haifar da komai ba sai karin wahala, akasin abin da jagoran APC yake nunawa.

A cewar Sule, tun farko APC bakarariya ce kuma babu abin da Muhammadu Buhari ya tsinanawa jama’a musamman na yankin Arewa.

Gwamnatin APC: SCSN ta zauna da Tinubu

An samu rahoto majalisar shari’a ta Najeriya SCSN, ta bayyana matsayarta a kan matakan da Bola Tinubu ya dauka bayan hawansa mulki.

Majalisar SCSN ta gabatarwa shugaban kasa takardar matsayar malamai, masana da kungiyoyi ta nemi a kawo saukin wahalar da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng