Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Tare da Ganduje da Shugabannin APC na Kano, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Tare da Ganduje da Shugabannin APC na Kano, Bayanai Sun Fito

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya labule da shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Kano
  • Daga cikin mahalarta ganawar dai har da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullaho Umar Ganduje da ɗan takarar gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna
  • Ganawar Shugaba Tinubu da jiga-jigan na jam'iyyar APC na zuwa ne bayan rashin nasarar da jam'iyyar ta yi a Kotun Ƙoli a hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - A ranar Alhamis Shugaba Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da tawagar da ta ƙunshi shugabannin jam’iyyar APC reshen jihar Kano a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja.

Jaridar The Punch ta ce jagororin tawagar akwai shugaban jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya isa fadar tare da rakiyar ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen gwamnan jihar da aka yi a ranar 18 ga Maris, Nasir Gawuna.

Kara karanta wannan

An barke da murnar nasarar Gwamna Abba a Kotun Koli, an tura muhimmin sako ga Kotun Koli

Shugaba Tinubu ya gana da Ganduje
Shugaba Tinubu ga sanya labule da Ganduje da Shugabannin APC na Kano Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Taron na ranar Alhamis ya zo ne mako guda bayan da Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin amincewa da babban abokin hamayyar Gawuna, Abba Yusuf na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me nene maƙasudin ganawar?

Ba a dai bayyana maƙasudin taron ba, sannan waɗanda suka halarci taron ba su yi magana da ƴan jaridar fadar shugaban ƙasa ba, rahoton Solacebase ya tabbatar.

A watan Maris ɗin shekarar 2024 da ta gabata ne dai mulki ya sauya hannu daga jam’iyyar APC a lokacin da Gawuna ya samu ƙuri’u 890,705 inda ya zo na biyu a bayan Gwamna Abba wanda ya samu ƙuri’u 1,019,602.

Ganduje Ya Bayyana Jihar da APC Za Ta Ƙwace a 2024

Shugaban All Progressives Congress (APC), Dakta Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa jam'iyya mai mulki ta fara shirye-shiryen kwato mulkin jihar Edo a 2024.

Ganduje ya yi wannan furucin ne a wurin taron masu ruwa da tsakin APC na jihar Edo da mambobin kwamitin gudanarwa na kasa da ya gudana a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng