Ana Tsaka da Ganawa Kan Matsalar Tikitin Musulmi da Musulmi, Tinubu Ya Nada Dan Arewa Babban Mukami

Ana Tsaka da Ganawa Kan Matsalar Tikitin Musulmi da Musulmi, Tinubu Ya Nada Dan Arewa Babban Mukami

  • Yayin da ake ta cece-kuce kan nade-naden Shugaba Tinubu, Bola ya sake muhimmin nadi daga Arewa
  • Tinubu ya nada Alhaji Aliyu Shehu Shinkafi daga jihar Zamfara a matsayin sakataren din-din-din a ma'aikatar ruwa
  • Wannan na zuwa ne yayin ake tsaka da ganawa da Majalisar Shari'ar Musulunci a birnin Abuja

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Tinubu ya nada Alhaji Aliyu Shehu Shinkafi a matsayin sakataren din-din-din a ma'aikatar albarkatun Ruwa.

Shinkafi wanda ya fito daga jihar Zamfara tuni ya fara aiki a ofishinsa da ke birnin Tarayyar Nigeria, Abuja.

Tinubu ya sake nadin shirgegen mukami a gwamnatinsa
Tinubu ya nada Shinkafi Sakataren din-din-din a ma'aikatar Ruwa. Hoto: Bola Tinubu, Aliyu Shinkafi.
Asali: Facebook

Waye Tinubu ya nada mukamin?

Shehu bayan shiga ofishin ya bukaci ma'aikatan hukumar da su ba da dukkan rayuwarsu ga ayyukan ci gaban kasa, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi halin Buhari 1 da ya burge shi, ya ce ya shammace shi bayan barin mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya godewa Shugaba Bola Tinubu kan wannan dama da ya bashi inda ya bukaci su hada kai don tsame shi a kunya.

Ya ce:

"Duk wanda ya himmatu wurin yin aiki tabbas zai zama kamar abokina a ko wane lokaci.
"Kuma a ko wane lokaci ina nan ga duk mai bukata ta sai dai ba na gulma ba.

Wane alkawari Shinkafi ya yi?

Shinkafi ya yabawa wanda ya gabace shi a kujerar, Didi Walson-Jack inda ya yi alkawarin ci gaba daga inda ya tsaya.

Shinkafi ya yi alkawarin aiki da babban Minista a ma'aikatar, Prof Joseph Utsev da karamin Minista, Muhammad Goronyo don kawo ci gaba.

Har ila yau, sakataren din-din-din a ma'aikatar, Walson-Jack daya bar kujerar ya koma ma'aikatar ilimi ta Tarayya, cewar Vanguard.

Walson-Jack ya godewa ma'aikatan kan irin goyon baya da suka ba shi yayin da ya ke rike da kujerar.

Kara karanta wannan

Reno Omokri ya jero manyan dalilai 9 da yasa mulkin Tinubu ya fi na Buhari

Tinubu ya amince da matakan rage farashin magani

A wani labarin, Shugaban kasa, Bola Tinubu ya amince da wasu kudurori guda uku da za su kawo sauyi a bangaren lafiya.

Matakan za su tallafa wurin rage farashin magani da yanzu ya fi karfin talaka.

Sauran hanyoyin sun hada da dakile yawan fita kasashen ketare da ma'aikatan ke yi da inganta ma'aikatan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.