Bola Tinubu Ya Rantsar da Shugaban PDP a Shirgegen Muƙamin Gwamnati, Ya Shiga Taron FEC a Villa

Bola Tinubu Ya Rantsar da Shugaban PDP a Shirgegen Muƙamin Gwamnati, Ya Shiga Taron FEC a Villa

  • Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da tsohon shugaban APC na jiha a matsayin kwamishinan hukumar tattara kuɗaɗen shiga RMAFC
  • Shugaban ƙasar ya yi haka ne jim kaɗan kafin fara taron majalisar zartarwa (FEC) a Aso Villa ranar Laraba, 17 ga watan Janairu, 2024
  • Desmond Akawor ya kasance shugaban jam'iyyar PDP na jihar Ribas har zuwa lokacin da Tinubu ya naɗa shi wannan muƙami tare da wasu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya rantsar da Ambasada Desmond Akawor a matsayin kwamishinan hukumar tattara kudaden shiga da rabon kudi (RMAFC).

Ambasada Akawor na ɗaya daga cikin mutanen da majalisar dattawan Najeriya ta amince da naɗinsu a matsayin kwamishinonin RMAFC a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ƴan bindigan da suka sace shugaban ƙaramar hukuma sun turo saƙo mai ɗaga hankali

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya rantsar da Akwor.
Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Akawor a Matsayin Kwamishinan RMAFC Hoto: Bayo Onanuga, Desmond Akawor
Asali: Twitter

Kafin wannan naɗi da shugaban ƙasa ya masa, Mista Akwor ya kasance shi ne shugaban jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta jihar Ribas, The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da bikin rantsuwar kama aikin kwamishinan hukumar ne jim kaɗan gabanin shiga taron majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Tinubu na jagorantar taron FEC na farko a 2024

An tattaro cewa bayan kammala rantsarwan ne shugaba Tinubu ya jagoranci taron FEC karo na farko bayan shigowar sabuwar shekara 2024.

Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, tare da wasu mambobin majalisar zartarwan sun halarci zaman na yau Laraba, 17 ga watan Janairu, 2024.

Daga cikin waɗanda aka hanga sun shiga taron baya ga SGF har da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, da mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribaɗu.

Kara karanta wannan

Kotun koli ta tanadi hukunci kan sahihancin nasarar gwamnan arewa, APC na tsaka mai wuya

Rahoton Vanguard ya nuna cewa Tinubu ya amince da yin taron FEC ranar Laraba ne sabida ranar Litinin ɗin da ta wuce ta haɗe da ranar tunawa da mazan fama.

Majalisa ta amince da dawo da tsaffin kwamishinoni a Ribas

A wani rahoton kuma Majalisar dokokin jihar Ribas ta kara tantance kwamishinoni 9 domin sake maida su kan muƙamai a gwamnatin Fubara.

Tsoffin kwamishinonin masu goyon bayan tsohon gwamna, Wike sun yi murabus ne yayin da rikicin siyasar jihar ya ɗauki zafi a watan Nuwamba, 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel