Abin Takaici Ne, Babban Lauya Ya Soki Abba Kabir da Gwamnoni Bayan Nasara a Kotun Koli, Akwai Dalili
- Gwamnan Kano da sauran gwamnonin da suka yi nasara a Kotun Koli sun sha suka bayan kalamansu
- Babban lauya a Najeriya, Inibehe Effiong ya soki gwamnonin bayan yabon Shugaba Tinubu kan nasararsu a Kotun Koli
- Wannan na zuwa ne yayin da mafi yawan gwamnonin suka yabawa Tinubu kan kokarinsa a shari'ar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Babban lauya a Najeriya, Inibehe Effiong ya soki gwamnonin da suka yi nasara a Kotun Koli.
Lauyan wanda ke zaune a Legas ya ce abin kunya ne yadda gwamnonin ke yabawa Shugaba Tinubu bayan sun samu nasara.
Mene lauyan ke cewa kan gwamnanonin?
Idan ba a mantaba, Gwamna Abba Kabir na Kano ya yabawa Tinubu kan irin kokarin tsame hannunsa a lamarin shari'ar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi da takwaransa na Plateau duk sun yabawa shugaban.
A ranar 12 ga watan Janairu ce aka yanke hukuncin zaben jihohi 8 da suka da da Kano da Bauchi da Plateau da Zamfara.
Sauran sun hada da Cross River da Legas da Ebonyi da kuma jihar Abia da ke Kudu kaso Gabashin kasar.
Ya ba su shawara kan imani da bangaren shari'a
Effiong ya ce abin mamaki ne yadda suka yi ta godewa Tinubu kamar alkalan Kotun Kolin don Tinubu suke yin hukunci.
Ya ce wannan ya tabbatar da cewa su kansu ba su yi imani da Kotun Koli ba idan aka barta ita kadai ta musu shari'a.
Ya ce:
"Wadannan gwamnoni da ke yabon Bola Tinubu bayan nasara a Kotun Koli ya tabbatar da cewa ba su da kwarin gwiwa kan kotun.
"Abin takaici ne yadda suke yabon Tinubu, shin su alkalan Kotun Kolin Tinubu suke yi wa aiki ne daman?."
Ya kara da cewa wannan ba shi ne hanyar da ya dace a nuna kwarin gwiwa kan hukumomi a kasar ba, cewar Leadership.
Abba ya shirya yaki kan wasu matsaloli 2
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya ce zai saka kafar wando da masu shan kwaya da kwacen waya.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ake ci gaba da murnar nasarar da ya samu a Kotun Koli.
Asali: Legit.ng