Kotun Koli Ta Jingine Hukunci Kan Shari'ar Zaben Neman Tsige Gwamnan Kaduna, Komai Na Iya Faruwa
- Kotun Koli ta shirya raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kaduna a Arewacin Najeriya
- Kotun ta jingine hukunci bayan jin bahasi daga dukkan bangarorin guda biyu da ke takaddama kan shari'ar
- Mai Shari'a, Kudirat Kekere-Ekun ta bayyana cewa za a sanar da su lokacin bayyana hukuncin shari'ar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kaduna da ake takaddama.
Kotun ta jingine hukuncin ne a bayan sauraran dukkan korafe-korafen bangarorin guda biyu da ke shari'ar, cewar Tribune.
Wane mataki kotun ta dauka kan shari'ar Kaduna?
Alkalan biyar karkashin jagorancin Mai Shari'a, Kudirat Kekere-Ekun ta bayyana cewa za a sanar da su lokacin bayyana hukuncin karshe kan shari'ar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Isa Ashiru Kudan na jam'iyyar PDP shi ke kalubalantar zaben Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC a zaben, cewar TheCable.
A baya, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC a matsayin halattaccen zababben gwamna a jihar.
Hukuncin da kotun ta yanke a bayan kan shari'ar Kaduna
Yayin hukunci, alkalan kotun guda uku sun yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Isa Ashiru Kudan saboda rashin gamsassun hujjoji.
Kudan har ila yau, ya sake daukaka kara zuwa Kotun Koli don neman kotun ta kwato masa hakkinsa da aka tauye.
Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, tun farko ta sanar da Gwamna Uba Sani a matsayin halastaccen gwamnan jihar a zaben da aka gudanar a watan Maris.
Kotun Koli ta shirya yanke hukunci a Gombe
A wani labarin makamancin wannan, Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci a zaben gwamnan jihar Gombe da ake takaddama a kai
Dan takarar jam'iyyar PDP, Muhammad Jibrin Barde shi ke kalubalantar zaben Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jami'yyar APC.
Kotun Daukaka Kara yayin hukuncinta ta tabbatar da nasarar Gwamna Inuwa Yahaya a matsayin gwamnan jihar a zaben da aka gudanar a watan Maris..
Asali: Legit.ng