An Barke da Murnar Nasarar Gwamna Abba a Jihar Nasarawa, An Tura Muhimmin Sako Ga Kotun Koli
- Ana cigaba da murnar nasarar da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya samu a Kotun Ƙoli kan Nasiru Gawuna
- Magoya baya da mambobin ƙungiyar Kwankwasiyya sun bi sahu wajen gudanar da nasu bikin a jihar Nasarawa
- Sun nuna farin cikinsu kan nasarar da gwamnan ya samu tare da yin kira da Kptum Ƙoli ta yi adalci a shari'ar zaɓen gwamnan Nasarawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Nasarawa - Mambobi da magoya bayan ƙungiyar Kwankwasiyya a ranar Laraba sun yi dandazo a ƙaramar hukumar Keana ta jihar Nasarawa.
Magoya bayan na ƙungiyar Kwankwasiyya sun taru ne domin murnar nasarar da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya samu a Kotun Ƙoli, cewar rahoton jaridar The Punch.
Da yake jawabi a ranar Laraba yayin bikin murnar nasarar da gwamnan ya samu, shugaban ƙungiyar a ƙaramar hukumar Keana ta jihar, Usman Dikko, ya yabawa shugaban ƙasa Bola Tinubu kan rashin tsoma bakinsa a hukuncin kotun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ƙara da cewa matakin da ya ɗauka zai taimaka wajen ƙarfafa dimokuradiyya a ƙasar nan, rahoton von.gov.ng ya tabbatar.
Wacce buƙata suka nema a wajen Kotun Ƙoli?
Ya kuma buƙaci Kotun Ƙoli ta yanke hukunci na gaskiya a rikicin zaɓen gwamnan jihar Nasarawa domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan jihar.
A kalamansa:
"Gwamnan jihar Kano cikakken ɗan Kwankwasiyya ne, shi ya sa muka taru domin murnar nasarar da ya samu a Kotun Ƙoli. Ko da yake an fuskanci ƙalubale a kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara, mun yi farin ciki da nasarar da ya samu daga ƙarshe.
"Muna so mu gode wa Shugaba Tinubu kan rashin tsoma baki a shari'ar da kuma barin wanda ya yi nasara a zaɓen ya zama shi ne ya yi nasara a kotun.
"Muna roƙon cewa kamar yadda alƙalan Kotun Ƙoli suka duba shari’ar jihar Kano da idon basira, su duba lamarin Jihar Nasarawa a tsanake, su tabbatar da nasarar wanda mutane suka zaɓa domin samar da zaman lafiya a jihar."
Jigon NNPP Ya Faɗi Dalilin Tinubu Na Ƙin Tsoma Baki a Shari'ar Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar NNPP ya bayyana dalilin da ya sanya Tinubu ya ƙi tsoma baki a shari'ar zaɓen gwamnan Kano.
Honorabul Danlami Kubau ya bayyana cewa shugaban ƙasan ya ƙi tsoma baki me saboda dimokuraɗiyyar ƙasar nan.
Asali: Legit.ng