An Shiga Uku a PDP, Mutumin Atiku Yana Barazanar Kai Shugabannin Jam’iyya Kotu

An Shiga Uku a PDP, Mutumin Atiku Yana Barazanar Kai Shugabannin Jam’iyya Kotu

  • Segun Showunmi zai dauki mataki domin ba zai juri yadda abubuwa suke cigaba da tafiya a PDP ba
  • ‘Dan siyasar ya nemi shugabannin PDP su kira taron NEC, kamar yadda dokar jam’iyyar adawa ta tanada
  • Lauyan Showunmi ya fadawa NWC cewa za ayi shari’a a kotu idan jam’iyya ta cigaba da sabawa dokarta

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Ogun - Segun Showunmi ya bukaci shugabannin jam’iyyar PDP na kasa su kira taron majalisar koli (NEC) ko kuwa ya dauki mataki.

Mista Segun Showunmi wanda ya nemi zama ‘dan takaran PDP a zaben gwamnan Ogun zai iya kai kara a kotu a cewar Daily Trust.

PDP..
Magoya bayan PDP Hoto: Official Peoples Democratic Party (PDP) Nigeria
Asali: Facebook

Segun Showunmi yana so PDP ta zauna

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun koma fada da juna, an tarwatsa yaran mashahurin ‘dan ta’adda

Tsohon ‘dan takaran yana so majalisar kolin jam’iyyar adawa ta PDP tayi zama domin a shawo kan matsalolin da suka bijiro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun Atiku Abubakar a zaben 2019 ya nuna muddin shugabannin PDP ba su zauna ba, doka za tayi aiki a kan su.

...an aikawa jam'iyyar PDP takarda

A wasikar da ya aikawa shugaban PDP na rikon kwarya ta hannun sakataren jam’iyyar, Segun Showunmi ya ce a kira taron NEC.

Punch tace lauyan da ya rubuta takardar gargadi a madadin Showunmi shi ne Anderson Asemota da ke aiki a Neplus Ultra Attorney.

Barista Asemota ya ce doka ta bukaci majalisar kolin jam’iyyar PDP watau NEC ta rika kiran taronta akalla duk bayan watanni uku.

Showunmi yake cewa rabon da ayi zaman NEC tun Satumban 2022 sa'ilin Iyiorcha Ayu yana rike da shugabancin jam’iyya na kasa.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 10, APC ta fadi wanda ya taimakawa Buhari ya samu takarar cin zabe

PDP ta ki yin zaman NEC tun 2022

Tun da jam’iyyar hamayyar ta shiga zaben 2023 da takarar gwamna a jihohin Bayelsa, Kogi da Imo, ya kamata a gabatar da rahoto.

A ra’ayin Showunmi, ana bukatar shugabannin jam’iyya su yi wa kwamitin NEC bayanin kudin da aka kashe da ayyukan da aka shirya.

Idan ana so PDP ta rayu a Najeriya, ‘dan siyasar ya ce dole a rika bin abin da doka ta ce, akasin haka zai sa shi ya shigar da kara gaban kotu.

Shugaban APC ya tona 'yan siyasa

A rahoton da aka samu a makon nan, an ji shugaban APC ya ce babbar matsalar hukumar INEC a wajen shirya zabe ita ce rashin tsaro.

Kowa zai ce laifin INEC ne ake samun matsala, amma Abdullahi Ganduje ya ce sharrin ‘yan siyasa ya jawo ake samun cibaya a zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng