Majalisar Dokokin Jihar PDP Ta Ɗauki Mataki Kan Kwamishinoni 9 da Suka Yi Murabus Daga Muƙamansu

Majalisar Dokokin Jihar PDP Ta Ɗauki Mataki Kan Kwamishinoni 9 da Suka Yi Murabus Daga Muƙamansu

  • Majalisar dokokin jihar Ribas ta kara tantance kwamishinoni 9 domin sake maida su kan muƙamai a gwamnatin Fubara
  • Tsoffin kwamishinonin masu goyon bayan tsohon gwamna, Wike sun yi murabus ne yayin da rikicin siyasar jihar ya ɗauki zafi a watan Nuwamba, 2023
  • Sai dai bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya, Fubara ya sake miƙa sunayensu ga majalisa domin tantance su a karo na biyu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Majalisar dokokin jihar Ribas ta sake tantancewa tare da wanke tsoffin kwamishinoni tara da suka yi murabus a baya domin maida su kan muƙamansu.

Majalisar dokokin ta amince wa Gwamna Siminalayi Fubara ya sake naɗa kwamishinonin a majalisar zartarwa ta jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya rantsar da shugaban PDP a shirgegen muƙamin gwamnati, ya shiga taron FEC a Villa

Majalisar Ribas ta tantance tsoffin kwamishinonin Wike 9.
Majalisar Dokokin Jihar Ribas Ta Amince da Kwamishinoni 9 a Majalisar Fubara Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto, Gwamna Fubara ya sake miƙa sunayen kwamishinonin guda 9, waɗanda suka yi murabus a watan Nuwamba, 2023 ga majalisar dokokin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinonin sun ɗauki matakin aje aiki ne a daidai lokacin da alaƙa ta yi tsami tsakanin Fubara da tsohon gwamnan da ya gabace shi, Nyesom Wike.

Idan zaku iya tunawa kwamishinoni 9 da wasu hadiman Fubara sun miƙa takardar murabus daga muƙamansu domin nuna goyon bayansu ga Wike, ministan Abuja.

Yadda majalisa ta ƙara tantance su a yau Laraba

An tattaro cewa majalisar dokokin ta sake tantance waɗan nan kwamishinoni masu goyon bayan Wike a karo na biyu a zaman yau Laraba, 17 ga watan Janairu, 2023.

Sai dai ƴan majalisar ba su yi wa tsofaffin kwamishinonin wata tambaya ba, kawai sun umarci su risinawa sandar majalisa ne su ƙara gaba, Daily Post ta tattaro.

Kara karanta wannan

Mutane na shan kebura, gwamnan PDP zai runtumo bashin N150bn kan muhimmin abu 1

Wannan mataki na zuwa ne bayan cimma yarjejeniya 8, wadda Gwamna Fubata ya rattaɓa wa hannu a wani taro da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya jagoranta a Villa.

Ganduje na shirin kwace Edo a 2024

A wani rahoton kuma Ganduje ya ce APC ta kudiri aniyar kara yawan jihohin da take mulki a Kudu maso Kudu ta hanyar kwace jihar Edo.

Shugaban APC na ƙasa ya ayyana cewa dama tun asali Edo ta jam'iyyar APC ce don haka zasu kwato ta a zaben gwamna a 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262