Bayan Rasa Kujerar Kano, Ganduje Ya Tafka Asara Bayan Shugaban APC Ya Yi Murabus, an Fadi Dalili
- Shugaban jam'iyyar APC a jihar Edo, Kanal David Imuse mai ritaya ya yi murabus daga kujerar shugabancin jam'iyyar
- Imuse ya yi murabus ne a karan kanshi ba tare da wata masala ba kamar yadda ya tabbatar a yau Talata
- Wannan na zuwa yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar Edo a ranar 21 ga watan Satumbar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben fidda gwani a jihar Edo, Shugaban jam'iyyar APC ya yi murabus.
Kanal David Imuse mai ritaya ya yi murabus ne a karan kanshi ba tare da wata masala ba kamar yadda ya ce.
Yaushe ya yi murabus a shugabancin APC?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata 16 ga watan Janairu a birnin Benin da ke jihar, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"Kamar yadda tsarin dokar jam'iyyar APC ya tabbatar a sashi na 31, na yi murabus a kujerar shugabancin jam'iyyar a karan kai na.
"Wannan murabus din na yi shi ne a karan kai na don tsayawa takarar gwamnan jihar a watan Satumba.
"Ina amfani da wannan dama in godewa dukkan masu ruwa da tsaki na wannan jam'iyya saboda damar da suka ba ni a jihar Edo."
Yaushe za a gudanar da zaben Edo?
Wannan na zuwa yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar Edo a ranar 21 ga watan Satumbar 2024.
Gwamna Obaseki Godwin na jihar zai karkare mulkinsa a karshen wannan shekara da muke ciki.
Mataimakinsa, Philip Shaibu shi ma ya nuna sha'awar tsayawa neman takarar gwamnan jihar a jam'iyyar PDP, cewar The Nation.
Gwamnan da mataimakinsa suna kai ruwa rana tun bayan nuna sha'awar Shaibu kan neman kujerar gwamnan jihar.
An samu hatsaniya a APC a Ondo
A wani labarin, An samu hatsaniya a jihar Ondo yayin da ake zaben fidda gwani a jihar don neman cike gurbi.
Dan tsohon Sifetan 'yan sanda a Najeriya, Ifeoluwa Ehindero shi ne ya yi nasarar lashe zaben a matsayin wanda zai yi takara a zaben.
Asali: Legit.ng