Bayan Shekaru 10, APC Ta Fadi Wanda Ya Taimakawa Buhari Ya Samu Takarar Cin Zabe
- Bisi Akande ya cika shekaru 85 a rayuwa, jam’iyyarsa ta APC ta fitar da jawabin taya shi murna
- APC ta ce tsohon shugaban na ta yana cikin manyan ‘yan kishin kasa kuma dattijo a Najeriya
- An tuno da yadda Akande ya taka rawar gani wajen kafa APC da kawo karshen mulkin jam’iyyar PDP
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta bayyana Bisi Akande a matsayin fitacce kuma kwararren tsohon ‘dan siyasa.
APC ta fitar da wani jawabi tana taya Cif Bisi Akande murnar cika shekara 85 a duniya, Daily Trust ta kawo rahoton ranar Talata.
APC: Bisi Akande ya cika 85
Sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwar Bisi Akande ta fito ne ta ofishin sakataren yada labaran APC na kasa, Felix Morka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barista Felix Morka ya ce dattijon ya yi fice wajen siyasar kawo cigaba kuma shi ya kafa tubalin nasarar APC a babban zaben 2015.
Sakataren yada labaran na APC ya ce tsohon gwamnan na jihar Osun ya kasance jagora da yake hada-kai tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyya.
Gudumuwar Bisi Akande a APC
A lokacin da aka yi wa APC rajista a shekarar 2013, tsohon gwamnan aka nada ya zama shugaban farko na rikon kwarya a tarihinta.
Daga baya aka yi zabe a 2014, John Odigie-Oyegun ya zama sabon shugaba na kasa.
"Dole APC ta godewa Cif Akande saboda dinbin gudumuwa mara adadi da ya bada wajen kafa jam’iyyar da shugabancinsa da ya shimfida nasara a babban zaben 2015.
"Uba, mai hada-kan jama’a kuma abin koyi, har gobe Cif Akande yana nan a matsayin jakadan zaman lafiya da sulhu a cikin jagorori da ‘ya ‘yan jam’iyyarmu."
- Felix Morka.
APC ta yabawa Bisi Akande
A karshe APC ta ce tana yi wa dattijo, ‘dan siyasa, shugaba kuma ‘dan kishin kasar murnar zagayowar rana irin ta yau a rayuwarsa.
An tuno da yadda Cif Akande ya taka rawar gani wajen kafa APC da doke jam’iyyar PDP
Shugabannin APC a tarihi
Cif John Odigie-Oyegun yana rike da majalisar aiwatarwa ta NWC ne Muhammadu Buhari ya lashe zaben shugaban kasa a 2015.
Tsohon sojan ya yi nasara ne bayan ya nemi kujerar ba tare da ya kai labari ba a zabukan da aka yi a 2003, 2007 da kuma 2011.
Bayan su an yi Adams Oshiomhole, Mai Mala Buni, Abdullahi Adamu da Abduallahi Ganduje wanda yanzu shi yake rike da NWC.
Asali: Legit.ng