Buhari ya taya Bisi Akande murnar cika shekaru 79 a duniya

Buhari ya taya Bisi Akande murnar cika shekaru 79 a duniya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hadu tare da dukkan mambobin jam’iyyar APC don taya tsaohon gwamnan jihar Osun Cif Adebisi Akande murnar cika shekaru 79 a duniya.

A wani jawabi da hadimin shugaban kasa, Mista Femi Adesina ya gabatar, shugaban kasar yana taya iyalai da abokan jigon jam’iyyar murnar falalar da Allah ya yiwa rayuwarsa.

Ya lissafo falalar wadanda suka hada da rawargani da ya nuna wajen jagoranci mai wahala don tabbatar da cewa al’ummanshi, da kasa baki daya sun anfana a rayuwa.

Buhari ya taya Bisi Akande murnar cika shekaru 79 a duniya
Buhari ya taya Bisi Akande murnar cika shekaru 79 a duniya

Jawabin yazo kamar haka, “A matsayina na abokinka, da kuma tunawa da zantukansu a baya, shugaban kasar ya yarda cewa jigon jam’iyyar APC wanda ya shiga harkar siyasa da wuri a rayuwa ya kasance mai shugabanci na Allah don ganin cewa kasar ta amfana da hikimarsa, basira da kuma muhimmin tanadi kamar yanda yake nunawa a shawarwari da yake gabatarwa akan al’amuran da suka shafi kasa.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun gurfanar da mai yiwa Buhari yakin neman zabe karo na biyu bayan ya caccaki hadiman shugaban kasa

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa Cif Akande ya bayar da gudunmawa kafawar cibiyoyin siyasa masu dinbin tarihi, kamar jam’iyyun UPN, AD, CAN, da jamiyya mai mulki wato APC, sannan kuma sun kasance manyan hanyoyi da hadaya wajen raya damokardiyya mai dorewa ga Najeriya wanda zuri’a zasu tuna da shi su kuma cigaba da nuna godiya.

“Shugaban kasar ya roki Allah da ya cigaba da raya Cif Akande cikin koshin lafiya, da basirar bauta ga kasarsa.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng