Kitumurmura Yayin da Majalisa Ta Gayyaci Kwamishinoni 9 da Suka Yi Murabus Don Sake Tantance Su
- Bayan yin murabus a mukamansu, kwamishinonin jihar Rivers za su dawo kujerunsu yayin da aka yi sulhu
- Majalisar jihar ta sake gayyatarsu don tantance su da kuma mayar musu da kujerunsu na mukamin kwamishina
- Wannan na zuwa ne bayan cimma yarjejeniya kan cewa dole a dawo da kwamishinonin mukamansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Majalisar jihar Rivers ta sake gayyatar kwamishinoni tara da suka yi murabus a jihar don tantance su.
Emeka Amadi, Magatakardar Majalisar shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Litinin 15 ga watan Janairu.
Mene dalilin murabus din kwamishinonin?
Idan ba a mantaba a kwanakin baya kwamishinoni da dama sun yi murabus daga mukaminsu a gwamnatin Siminalayi Fubara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Murabus din nasu na da alaka da rashin jituwa tsakanin gwamnan da mai gidansa, Nyesom Wike a jihar, cewar Channels TV.
Sai dai a cikin sharudan zaman lafiya da aka kulla wanda Shugaba Tinubu ya jagoranta akwai dawo da kwamishinonin mukaminsu a jihar.
Majalisar karkashin jagorancin Hon. Hon Martin Amaewhule ta gayyace su ne don mayar musu da kujerunsu bayan tantance su.
Yaushe za a sake tantance kwamishinonin?
Sanarwar ta ce:
"Majalisar jihar Rivers ta na gayyatar wadannan kwamishinoni don tantance su a matsayinsu na mambobin zartarwa a jihar."
Kwamishinonin sun hada da:
1. Zacchaeus Adangor SAN
2. Dakta Jacobson Mbina
3. Dakta Gift Worlu
4. Inime Chinwenwo- Aguma
5. Injiniya Chukwuemeka Woke
6. Farfesa Prince Chinedu Mmom
7. Dakta George-Kelly D. Alabo
8. Hon. Isaac Kamalu
9. Injiniya Austin Ben Chioma.
Za a gabatar da tantancewar a ranar Laraba 17 ga watan Janairu a misalin karfe 10 na safe a harabar Majalisar da ke Port Harcourt, cewar Leadership.
Har ila yau, sanarwar ta bukaci wadanda za a tantance din su zo da takardunsu don binciken kwa-kwaf.
Wike ya tura sako ga Fubara kan 2027
A wani labarin, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya sake caccakar Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.
Wike ya ce ya kamata a bari sai zaben 2027 ya zo a nan za a gane waye ne sama da wani a tsakaninsu.
Asali: Legit.ng