Nasara a Kotun Koli: Abba Gida-Gida Ya Samu Kyakkyawar Tarba Yayin da Ya Koma Kano Ta Hanyar Kaduna
- Masoyan Abba Gida-Gida da masu yi masa fatan alkhairi sun yi tururuwa a jihar Kaduna don taya shi murna bayan hukuncin Kotun Koli
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zabi bin mota daga Abuja zuwa jihar Kano bayan halartan zaman kotun da ta tabbatar da nasararsa, inda a nan ne ya ratsa ta jihar Kaduna
- Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar jiharsa suka taru a Kwanar Dangora don tarbansa inda daga nan za su yi masa rakiya har zuwa gidan gwamnatin Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Dandazon magoya bayan jam'iyyar NNPP da yan Kwankwasiyya sun yi tururuwan fitowa a jihar Kaduna yayin da ayarin motocin Gwamna Abba Kabir Yusuf suka zo wucewa.
Abba Gida-Gida wanda ya kasance daya daga cikin gwamoni hudu da suka halarci zaman Kotun Koli a Abuja gabannin yanke hukuncin karshe a shari'o'in zaben gwamnoni, ya zabi bin hanyar mota zuwa Kano, rahoton Daily Trust.
Gwamnan ya isa jihar Kaduna da ke makwabtaka da Kano inda ayarin motocinsa suka yi kicibis da dandanzon jama'a cike da titi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana sa ran dubban magoya baya da masu fatan alkhairi za su tarbi gwamnan a Kwanar Dangora inda daga nan za su yi masa rakiya har zuwa gidan gwamnati.
Daya daga cikin magoya bayansa mai suna Nasiru Muhammad ya ce:
"Dole mu kunsa masu (yan adawa) irin bakin cikin da suka so kunsa mana ko ma fiye da haka. Sun yi shirin haka idan suka yi nasara, amma Allah ne mai iko.
"Bangaren shari'a sun yi abun da ya dace kuma gaskiya ta yi halinta. Za mu yi maraba da gwamnan al'umma, zabinsu kuma wanda muka zaba.
"Ba a ji ta da sauki ba a yan watannin nan da suka wuce kuma wannan dalilin da yasa dole mu nuna masa soyayya a yau."
Legit Hausa ta zanta da wani masoyin Abba mai suna Muhammad Rabi'u inda ya ce lallai gwamnan ya cancanci duk wani soyayya da ake masa.
"Allah ne ya ba Abba farin jini ba wai a nan Kano kadai ba, harma da sauran sassa na kasar. Ya cancanci a nuna masa murna a irin wannan lokaci duba ga gwagwarmayar da ya sha kafin ya tabbata a kan kujerarsa.
"An so yi masa fashin kuri'unsa amma Allah bai nufa ba kin ga kuwa dole a taya shi lale. Masoya kan yana da ita ta ko'ina kuma muna yi masa addu'ar Allah ya sa ya dawo a sa'a. Amin."
Abba Gida-Gida ya kafa zauren dattawan Kano
A wani labarin, mun ji a baya cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa zauren dattawan jihar Kano domin ta zamo wata majalisa mai ba gwamnati shawara, rahoton Punch.
Wannan ci gaban na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Dawakin Tofa, ya gabatarwa manema labarai a ranar Asabar, 15 ga watan Janairu, rahoton The Sun.
Ya bayyana cewa Allah ya albarkaci jihar da tarin dattawa da tsoffin shugabanni wadanda suka da suka samu nasarar gudanar da ayyukansu kuma ci gaba da kasancewa cikin koshin lafiya.
Asali: Legit.ng