Jigon NNPP Ya Bayyana Dalili 1 Da Ya Sanya Tinubu Kin Tsoma Baki a Shari'ar Zaben Gwamnan Kano
- An ji dalilin ƙin tsoma bakin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a shari'ar zaɓen gwamnan Kano daga bakin wani jigon NNPP
- Ibrahim Danladi Kubau ya bayyana cewa shugaban ƙasa bai sanya baki domin APC a shari'ar ba ne saboda mutanen Kano sun yi watsi da jam'iyyar
- Ibrahim ya bayyana hukuncin Kotun Kolin a matsayin babbar nasarar ga dimokuraɗiyyar Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Wani jigo a Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Honorabul Ibrahim Danlami Kubau, ya yi magana kan hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan shari'ar zaɓen gwamnan Kano.
Honorabul Danlami ya yi takarar kujerar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Ikara da Kubau, a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar NNPP a babban zaɓen 2023.
A yayin wata tattaunawa da Legit Hausa, Danlami ya nuna farin cikinsa kan hukuncin da Kotun Kolin ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf, matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana hukuncin a matsayin babbar nasara ga dimokuraɗiyyar Najeriya, domin ya ceto ta daga faɗa wa cikin ruɗani.
Ya nuna cewa da Kotun Kolin da amince da hukuncin da kotun zaɓe da Kotun Daukaka Kara, suka yi na soke ƙuri'un da APC ta yi zargin ba ingantattu ba ne, da ta buɗe ƙofar da wasu za su iya yin hakan a nan gaba.
Me ya hana Tinubu sanya baki a shari'ar Kano?
Da aka tambaye shi ko meyasa Shugaba Tinubu bai tsoma baki domin APC ba a shari'ar zaɓen ba, sai ya kada baki yace:
"Ba maganar APC ba ne, magana ce ta Najeriya, ƴan Najeriya da dimokuraɗiyya, mutane sun riga da sun san abin da suke so, ba zai iya sanya baki domin APC ba saboda al'ummar Kano sun riga da sun yi watsi da APC"
"Ba zai iya sanya baki domin APC a Kano ba domin tuntuni mutanen Kano sun sauka daga layin APC, mutane suna son sabuwar fuska, mai sabon tsari da sabon fata, wanda hakan ne ya sanya suka zaɓi wasu ƴan takara a Kano, Bauchi, Zamfara da wasu sauran jihohin."
Gawuna Ya Amince da Hukuncin Kotun Ƙoli
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna, ya yi martani kan rashin nasararsa a kotun ƙoli.
Gawuna ya bayyana ya amince da hukuncin wanda ya tabbatar da nasarar Gwamna Abba na jam'iyyar NNPP.
Asali: Legit.ng