Duk da Nasarar da Su Ka Samu, Tsohon Gwamnan Arewa Ya Soki Kotu Kan Wani Hukunci a Jiharsa
- Jonah Jang, tsohon gwamnan jihar Plateau ya caccaki hukuncin Kotun Daukaka Kara a zaben 'yan Majalisu
- Jang ya bayyana hukuncin da ya rusa 'yan Majalisun PDP a jihar na Tarayya da jihohi a matsayin rashin adalci
- Ya ce tabbas dole hukumomi su sake zama don tabbatar wa jama'a abin da su ka zaba a yayin zabe a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Tsohon gwamnan jihar Plateau, Janah Jang ya soki hukuncin Kotun Daukaka Kara a hukuncinta a jihar.
Jang ya ce hukuncin da ya rusa 'yan Majalisun PDP a jihar na Tarayya da jihohi a matsayin rashin adalci.
Mene Jang ke cewa kan hukuncin kotu?
Tsohon gwamnan wanda ya taba rike kujerar Sanata mai wakiltar Plateau ta Arewa ya ce hukuncin fashi ne ga 'yancin al'ummar jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ya biyo bayan hukuncin Kotun Daukaka Kara da ta kwace dukkan kujerun Tarayya da na jihohi a jihar.
Matakin na kwace dukkan kujerun 'yan Majalisun PDP ya biyo bayan zargin rashin tsari na jam'iyyar inda ta ki gudanar da babban taronta a jihar.
Sanatan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Kwamred Clinton Garuba ya fitar, cewar Leadership.
Wane roko ya tura ga kotun?
Ya bukaci kotun ta sake duba hukuncin shari'ar zabukan 'yan Majalisun tare da sake daukar mataki a kai.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar Plateau ta shigar da Hukumar Shari'a a kasar kara don sake duba kan shari'ar.
Ya ce:
"Wannan hukunci ya saba doka bayan ayyana su a matsayin 'yan Majalisu wadanda suka gagara cin zabe."
Jang ya ce dole mahukunta su bai wa mutane abin da suka zaba inda ya ce za su ci gaba da goyon bayan Gwamna Caleb Mutfwang.
Ya ce Caleb a cikin watanni takwas ya yi abin da tsohon gwamnan jihar, Simon Lalong ya yi a cikin tsawon shekaru takwas, cewar Daily Post.
Kotun Koli ta yi hukunci a zaben Plateau
A wani labarin, Kotun Koli ta raba gardama a shari'ar zaben gwamnan jihar Plateau a jiya Juma'a a Abuja.
Kotun ta ayyana Gwamna Caleb Mutfwang a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar a zaben da aka gudanar.
Asali: Legit.ng