“Ai Baka Sani Ba Ko Shi Ne Ya Bada Sunan Ali Nuhu”, Bashir Ahmad Ga Mai Sukar Rarara

“Ai Baka Sani Ba Ko Shi Ne Ya Bada Sunan Ali Nuhu”, Bashir Ahmad Ga Mai Sukar Rarara

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Ali Nuhu cikin daraktoci a ma'aikatar fasaha, al'adu da tattalin arzikin fikira a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu
  • Masu amfani da soshiyal midiya da dama sun taya shi murnar samun wannan mukami, yayin da wasu suka yi wa mawaki Dauda Kahutu Rarara shagube kan rashin samun mukami
  • Sai dai tsohon hadimin Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya kare shi, inda ya ce watakila Rarara ne ya mika sunan Ali Nuhu gaban shugaban kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

A ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu ne Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabbin daraktoci 11 a ma'aiktar fasaha, al'adu da tattalin arzikin Fikira.

Daga cikin wadanda suka samu shiga a matsayin daraktocin ma'aikatar harda fitaccen jarumin masana'antar shirya fina-finan Hausa, Ali Nuhu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Nada Ali Nuhu Mukamin Shugaban Hukumar Fina-Finai ta Najeriya

Bashir ya kare Rarara kan mukamin da aka ba Ali Nuhu
“Ai Baka Sani Ba Ko Shi Ne Ya Bada Sunan Ali Nuhu”, Bashir Ahmad Ga Mai Sukar Rarara Hoto: Hoto: @BashirAhmaad/X, Ali Nuhu, Dauda Kahutu Rarara/Instagram
Asali: UGC

Tun bayan nada Sarki Ali kan wannan mukamin, an samu yan taya murna da masu yi martani daban-daban kan wannan kujera da ya samu na shugaban cibiya fina-finai na Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mai amfani da dandalin X, @jibreelKhalil, ya yi shagube ga fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahuru Rarara kan wannan mukami da aka bai wa Ali ba shi ba.

A cewar matashin, Rarara na nan a wani wuri cikin fushi, yana mai cewa bambancin wanda ya yi karatu da wanda bai yi ba kenan.

"Nada Ali Nuhu a matsayin Manajan Darakta, cibiyar fina-finai na Najeriya labari ne mai dadi. Ina fatan ganin gagarumin ci gaba a karkashin shugabancinsa.
"Na san Kahutu Rarara na nan a wani wuri cikin fushi. Wannan shine bambanci tsakanin ilimi da nuna girman kai."

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 7 da Tinubu ya aiwatar a cikin kwanaki 7 na shekarar 2024, in ji Onoh

Bashir Ahmad ya kare mawaki Rarara

Sai dai kuma, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya kare Rarara a kan wannan batu, inda ya ce aka sani ko shi ne ya gabatar da sunan Ali Nuhun don a ba shi mukamin.

Bashir ya rubuta a shafinsa na X:

"To ai baka sani ba ko shi ne ya bada sunan Ali Nuhun, tunda a tunanin shi idan ba a bashi minister ba to ya kamata a zauna dashi don tantance wadanda ya kamata a bawa din."

Tinubu ya nada daraktoci 11 a ma'aikatar al'adu

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin daraktoci 11 a ma'aikatar Fasaha, Al'adu da Tattalin Arzikin Fikira.

Wadannan daraktoci za su shugabanci hukumomi daban-daban a karkashin ma'aikatar, ciki harda hukumar tace fina-finai ta kasa, da kuma gidan tarihi na kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel