“Ai Baka Sani Ba Ko Shi Ne Ya Bada Sunan Ali Nuhu”, Bashir Ahmad Ga Mai Sukar Rarara
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Ali Nuhu cikin daraktoci a ma'aikatar fasaha, al'adu da tattalin arzikin fikira a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu
- Masu amfani da soshiyal midiya da dama sun taya shi murnar samun wannan mukami, yayin da wasu suka yi wa mawaki Dauda Kahutu Rarara shagube kan rashin samun mukami
- Sai dai tsohon hadimin Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya kare shi, inda ya ce watakila Rarara ne ya mika sunan Ali Nuhu gaban shugaban kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
A ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu ne Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabbin daraktoci 11 a ma'aiktar fasaha, al'adu da tattalin arzikin Fikira.
Daga cikin wadanda suka samu shiga a matsayin daraktocin ma'aikatar harda fitaccen jarumin masana'antar shirya fina-finan Hausa, Ali Nuhu.

Source: UGC
Tun bayan nada Sarki Ali kan wannan mukamin, an samu yan taya murna da masu yi martani daban-daban kan wannan kujera da ya samu na shugaban cibiya fina-finai na Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mai amfani da dandalin X, @jibreelKhalil, ya yi shagube ga fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahuru Rarara kan wannan mukami da aka bai wa Ali ba shi ba.
A cewar matashin, Rarara na nan a wani wuri cikin fushi, yana mai cewa bambancin wanda ya yi karatu da wanda bai yi ba kenan.
"Nada Ali Nuhu a matsayin Manajan Darakta, cibiyar fina-finai na Najeriya labari ne mai dadi. Ina fatan ganin gagarumin ci gaba a karkashin shugabancinsa.
"Na san Kahutu Rarara na nan a wani wuri cikin fushi. Wannan shine bambanci tsakanin ilimi da nuna girman kai."

Kara karanta wannan
Muhimman abubuwa 7 da Tinubu ya aiwatar a cikin kwanaki 7 na shekarar 2024, in ji Onoh
Bashir Ahmad ya kare mawaki Rarara
Sai dai kuma, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya kare Rarara a kan wannan batu, inda ya ce aka sani ko shi ne ya gabatar da sunan Ali Nuhun don a ba shi mukamin.
Bashir ya rubuta a shafinsa na X:
"To ai baka sani ba ko shi ne ya bada sunan Ali Nuhun, tunda a tunanin shi idan ba a bashi minister ba to ya kamata a zauna dashi don tantance wadanda ya kamata a bawa din."
Tinubu ya nada daraktoci 11 a ma'aikatar al'adu
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin daraktoci 11 a ma'aikatar Fasaha, Al'adu da Tattalin Arzikin Fikira.
Wadannan daraktoci za su shugabanci hukumomi daban-daban a karkashin ma'aikatar, ciki harda hukumar tace fina-finai ta kasa, da kuma gidan tarihi na kasa.
Asali: Legit.ng
