Zaben 2027: Jam'iyyar PDP Ta Karaya, Ta Bayyana Babbar Fargabar da Take Yi Kan Kawar da APC
- Jam'iyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta yi magana kan yiwuwar ƙwace mulki a hannun jam'iyyar APC
- Jam'iyyar ta bayyana cewa idan har ba haɗaka jam'iyyun adawa suka yi ba, zai yi wuya a iya kawar da APC daga mulki
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar shi ne ya yi kiran da jam'iyyun adawan da su zo a yi haɗaka
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa zai yi wuya a rusa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen shugaban lasa na 2027 ba tare da haɗaka ta gaskiya ba.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya gabatar da kuɗurin haɗaka, yayin da ya karɓi baƙuncin kwamitin zartarwa na majalisar ba da shawara ta jam'iyyu ta Najeriya.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi gargaɗi kan yiwuwar Najeriya zama ƙarƙashin mulkin jam’iyya ɗaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Duk mun ga yadda APC ke ƙara mayar da Najeriya mulkin kama-karya na jam’iyya ɗaya. Idan ba mu taru mun ƙalubalanci abin da jam’iyya mai mulki ke ƙoƙarin haifarwa ba, dimokuraɗiyyar mu za ta sha wahala, kuma sakamakon hakan zai shafi waɗanda ba a haifa ba."
Mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar PDP, Ibrahim Abdullahi, wanda ya bayyana haka a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Punch, ya ce Atiku ya yi wannan kiran ne domin kare makomar Najeriya da ƴan Najeriya.
Wane kira jam'iyyar PDP ta yi?
Abdullahi wanda ya yi zargin cewa APC ta talauta ƴan Najeriya, ya ce haɗakar jam’iyyun adawa na gaskiya ne kaɗai za su iya korar gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu.
A kalamansa:
"Mun yi imanin haɗewa ko haɗa kan dukkan jam’iyyun adawa zai haifar da kyakkyawan sakamako. Don haka akwai buƙatar sauran jam’iyyun siyasa su fahimci cewa zai yi wahala a kayar da jam’iyyar All Progressives Congress ba tare da haɗaka ba.
"Don haka dole ne sauran jam’iyyun siyasa su ga dalilin su kuma gane hakimar jam’iyyar PDP na kiran yin haɗaka. Don haka, idan sun ga haka, to mafi alheri ga ƴan adawar Najeriya da jama’a.
"Amma idan sauran jam’iyyun siyasa suna son su yi tafiya su kaɗai, ba su kai PDP ƙarfi ba. Yana da matuƙar wahala a garemu mu cimma manufar ɗaukar nauyin gwamnati tare da korar wannan rundunar mamaya da ta yanke shawarar zaluntar ƴan Najeriya da gana musu mafi girman azaba da baƙin ciki.”
Atiku Ya Faɗi Shirinsa Kan APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi magana kan nasarar gwamnoni a kotun koli.
Atiku ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin jan ragamar gamayyar jam'iyyun adawa wajen yaƙar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da APC mai mulki a 2027.
Asali: Legit.ng