Kotun Koli Ta Ƙara Yanke Hukunci Kan Sahihancin Nasarar Gwamnan Adawa, PDP Ta Yi Warwas
- Kotun koli ta yanke hukunci kan ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta na gwamna suka kalubalanci nasarar gwamnan Abia
- A zaman yanke hukuncin yau Jumu'a, 12 ga watan Janairu, kotun ta kori ƙarar gaba ɗaya bisa rashin cancanta
- Wannan hukunci na zuwa ne bayan kotun ta bayyana matsayarta kan zaben gwamnonin jihohin Zamfara, Kano da Filato
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia - Kotun kolin Najeriya ta kori karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamnan suka ƙalubalanci sakamakon zaben gwamnan jihar Abia na 2023.
Jam'iyyar PDP da ɗan takararta, Okechukwu Ahiwe, sun shigar da ƙarar ne suna neman kotu ta tsige Gwamna Alex Otti na jam'iyyar Labour Party daga kujerar gwamna.
Kano: Gwamna Abba ya maida martani bayan kotun ƙoli ta yanke hukunci, ya gode wa wanda ya ba shi nasara
A hukuncin da ta yanke mintuna kaɗan da suka wuce, kotun koli ta bayyana cewa ƙarar ba ta da tushe watau ba ta cancanta ba kuma nan take ta kori ƙarar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar The Nation ta tattaro cewa mai shari'a Uwani Abba-Aji ce ta karanto hukuncin a zaman ƙarshe yau Jumu'a, 12 ga watan Janairu, 2023.
Kotun koli ta kori ƙarar PDP da Ahiwe
Mai shari’a Uwani Abba-Aji ta ce wadanda suka shigar da kara (Ahiwe da PDP) sun kasa tabbatar da cewa Otti bai cancanta ya tsaya takara ba, kuma zaben cike yake da maguɗi.
Ba tare da ɓata lokaci ba, Alkalin ta wuce kai tsaye ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamna da kotun ɗaukaka ƙara, waɗanda suka ba Otti nasara.
A halin yanzu dai kotun ta fara karanto hukuncinta a karar da jam’iyyar APC da dan takararta na gwamna, Ikechi Emenike suka shigar kan zaben Gwamna Otti.
Gwamnonin jihohin Zamfara, Kano, Filato, Bauchi, da Ebonyi duk sun samu nasara a gaban kotun koli yau Jumu'a, cewar rahoton Channels Tv.
Dauda Lawal ya yi nasara kan Matawalle
A wani rahoton kuma Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da Gwamna Dauda Lawal a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben jihar Zamfara a watan Maris
Kotun ta soke hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na ayyana zaben gwamnan a matsayin wanda bai kammala ba.
Asali: Legit.ng