Kotun Koli Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Neman Kifar da Gwamna APC, Ta Bayyana Dalilai
- Yayin da aka yanke hukuncin zaben gwamnoni da dama a Abuja, Kotun Koli ta raba gardama a zaben jihar Cross River
- Kotun ta tabbatar da Gwamna Bassey Otu na jami'yyar APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar
- Har ila yau, kotun ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Sandy Onor saboda rashin gamsassun hujjoji
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun Koli da ke birnin Tarayya Abuja ta yi hukunci kan zaben gwamna jihar Cross River.
Kotun ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Sandy Onor saboda rashin gamsassun hujjoji.
Wane hukunci kotun ta yanke kan shari'ar?
Har ila yau, ta ayyana Gwamna Bassey Otu a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar, TheCable ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar INEC ta tabbatar da Bassey Otu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka gudanar a watan Maris.
Yayin hukuncin, Mai Shari'a, Helen Ogunwumiju ya ce wannan korafi ba ya da tushe kuma ba ta wa bangaren shari'a lokaci ne.
Wane hukunci aka yanke a watan Satumba a jihar?
Sai dai a watan Satumbar 2023, Otu ya sha kaye a hukuncin kotun sauraran kararrakin zabe jihohi da aka gudanar.
Otu ya samu nasarar zaben gwamnan jihar da kuri'u 258,619 a kananan hukumomi 15 daga cikin 18 da ke jihar.
Yayin da dan takarar jam'iyyar PDP, Onor da ke biye da shi a matsayin na biyu ya samu kuri'u 179,636 a zaben, kamar yadda Channels TV ta tattaro.
Kotu ta yi hukunci a zaben Cross River
A wani labarin, Kotun Daukaka Kara ta raba gardama kan tababar da ake yi a shari'ar zaben gwamnan jihar Cross River.
Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Bassey Otu na jam'iyyar APC a matsayin zababben gwamnan jihar da aka gudanar a watan Maris.
Har ila yau, Kotun ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Sandy Onor saboda rashin hujjoji.
Asali: Legit.ng