Yanzun Nan: Abba Gida-Gida da Wasu Gwamnoni 3 Sun Isa Kotun Koli Gabannin Yanke Hukunci

Yanzun Nan: Abba Gida-Gida da Wasu Gwamnoni 3 Sun Isa Kotun Koli Gabannin Yanke Hukunci

  • Kotun Kolin Najeriya da ke zama a babban birnin tarayya Abuja ta fara cikar kwari gabannin yanke hukunci kan zabukan gwamnoni takwas
  • Zuwa yanzu, Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano, Bala Mohammed na Bauchi, Dauda Dare na Zamfara da Caleb Mutfwang na Filato duk sun hallara a babbar kotun
  • Hukuncin da Kotun Kolin za ta yanke a yau Juma'a, 12 ga watan Janairu, shine zai kawo karshen takaddamar zabukan gwamnonin wadannan jihohi

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abuja - Yayin da Kotun Koli ke shirin yanke hukunci kan takaddamar zabukan wasu gwamnonin jihohi, a kalla gwamnoni hudu ne suka isa babbar kotun don zaman hukuncin.

Gwamnoni hudu da suka isa Kotun Kolin sune Bala Mohammed na jihar Bauchi, Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, Caleb Mutfwang na jihar Filato da kuma Dauda Lawal na jihar Zamfara, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Ciki ya duri ruwa yayin da ake saura awanni kadan a yanke hukunci a Kano da Zamfara da jihohi 6

Gwamnonin Zamfara, Filato, Kano da Bauchi sun isa Kotun Koli
Yanzun Nan: Abba Gida-Gida da Wasu Gwamnoni 3 Sun Isa Kotun Koli Gabannin Yanke Hukunci Hoto: Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar
Asali: Twitter

Simon Lalong, tsohon gwamnan jihar Filato ma ya hallara a Kotun Kolin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana sa ran babbar kotun za ta yanke hukunci kan shario'in zabukan gwamnoni a jihohi takwas, da suka hada da Legas, Filato, Bauchi, Kano, Abia, Zamfara da Cross River.

Kotun daukaka kara ta tsige Gwamna Yusuf na Kano a baya kan hujjar cewa shi ba dan jam’iyyar NNPP bane.

Yaya ake ciki a jihar Kano?

Mun dai kawo a baya cewa an tsaurara matakan tsaro yayin da ake zaman dar-dar a jihohin Kano da Zamfara da Plateau da sauransu.

A jihar Kano wacce ita ce shari’ar da tafi daukar hankulan ‘yan Najeriya gaba daya, Daily Trust ta tattaro cewa ana ta zaman dar-dar da cece-kuce kan shari’ar.

Yayin da ake cikin wannan hali, Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Hussaini Gumel ya ce sun shirya tsaf don dakin tashin-tashina a jihar.

Kara karanta wannan

Yusuf vs Gawuna: Sabon hasashe ya nuna wanda zai yi nasara a Kotun Koli a shari'ar Kano

Malamin Musulunci ya yi hasashe

A baya mun ji cewa babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil ya ce zai yi wahala jam'iyyar NNPP ta yi nasara a kotun koli.

Shehin malamin ya ja hankalinsu da su daukaka kara don samun damar lokacin da za su tsara barin gidan gwamnati, cewar Leadership Hausa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng