Kotun Koli Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Takaddamar Zaben Gwamnan PDP, NNPP Ta Gurza Kasa

Kotun Koli Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Takaddamar Zaben Gwamnan PDP, NNPP Ta Gurza Kasa

  • Yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli da dama a Najeriya, jihar Akwa Ibom ta san matsayinta kan takaddamar zabe
  • Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Umo Eno a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar babu tantama
  • Har ila yau, kotun ta yi fatali da korafe-korafen 'yan takarar jam'iyyun APC da YPP da kuma NNPP a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Akwa Ibom, cewar The Nation.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Umo Eno na jami'yyar PDP a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan PDP
Kotun Koli ta yi hukunci a zaben gwamnan jihar Akwa Ibom. Hoto: Umo Eno.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke?

Kara karanta wannan

Kujerar gwamnan APC na tangal-tangal, kotun ƙoli ta tanadi hukunci kan zaɓen da ya ci a 2023

Yayin hukuncinta, kotun ta yi fatali da korafe-korafen jam'iyyun APC da YPP da kuma NNPP saboda rashin gamsassun hujjoji da suka gabatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan Kotun Daukaka Kara a baya ta tabbatar da nasarar gwamnan a matsayin zababben gwamna halastacce, cewar TVC News.

Daga bisani 'yan takarar jam'iyyun sun daukaka kara don kalubalantar hukuncin kotun wanda bai musu dadi ba da cewa akwai kura-kurai.

Alkalan biyar karkashin jagorancin Mai Shari'a, Uwani Abba-Aji sun yi fatali da korafin dan takarar jam'iyyar APC, Akanimo Udofia.

Matakin da masu korafin suka dauka

Har ila yau, sun yi watsi da korafin dan jam'iyyar YPP, Albert Bassey da kuma NNPP, John Udoedehe.

Lauyoyin dukkan masu korafin sun janye korafe-korafensu bayan kotun ta ce ba su da hujjoji kwarara.

Masu korafe-korafen su na kalubalantar zaben Eno kan zargin gabatar da takarar kammala sakandare ta jabu ga hukumar INEC.

Kara karanta wannan

APC ta bayyana babban dalilin da ya sa ta ke samun nasara a zabuka, ta yi alkawari ga 'yan kasa

Kotun Koli ta tanadi hukunci kan zaben jihar Ogun

A wani labarin, Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Ogun.

Kotun ta yi hukunci ne yayin da dan takarar jam'iyyar PDP, Oladipopu Adebutu ke kalubalantar zaben Gwamna Dapo Abiodun na APC.

A baya, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Dapo Abiodun na APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel