Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci Kan Shari'ar da Ke Barazana Ga Gwmnan APC, Akwai Kura-kurai

Kotun Koli Ta Tanadi Hukunci Kan Shari'ar da Ke Barazana Ga Gwmnan APC, Akwai Kura-kurai

  • Kotun Koli ta shirya raba gardama a shari'ar zaben gwamnan jihar Ogun da ake takaddama a kai bayan sanar da sakamakon zabe
  • Tun farko, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Dapo Abiodun na jam'iyyar APC
  • Yayin da dan takarar jam'iyyar PDP, Oladipopu Adebutu ke kalubalantar zaben da cewa an yi kuskuren sanar da sakamakon

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Ogun, cewar Channels TV.

Kotun ta dauki matakin ne bayan karar da dan takarar jam'iyyar PDP, Oladipupo Adebutu ya shigar da ya ke kalubalantar zaben.

Kotun Koli ta tanadi kan shari'ar zaben gwamnan APC
Kotun Koli ta tanadi hukunci kan zaben jihar Ogun. Hoto: Dapo Abiodun, Oladipopu Adebutu.
Asali: Twitter

Wane hukunci kotun ta yanke?

Tun farko, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Dapo Abiodun na jam'iyyar APC, TVC News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Nesa ta zo kusa: Kotun koli ta sanya ranar yanke hukuncin kan zaben gwamnan Kano, Bauchi da wasu jihohi 5

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gungun Alkalan guda biyar karkashin jagorancin Mai Shari'a, John Okoro sun tanadi hukunci bayan dukkan bangarorin sun gabatar da korafe-korafensu.

Adebutu na bukatar kotun da fatali da zaben da APC ta yi nasara bayan INEC ta soke zaben rumfuna 99 wanda ta bukaci a sake zabe a wuraren.

Duk da soke zaben da ta yi, INEC ta kuma sanar da Abiodun a matsayin wanda ya lashe zaben ba tare da kula da ratar sa ke tsakani ba.

Mene korafin Adebutu kan zaben?

Gwamnan ya ci zabe da ratar kuri'u dubu 13 yayin da rumfunan da aka soke sun kai kuri'u sama da dubu 44.

Adebutu ya sha kaye tun a zaben yayin da kotun sauraran kararrakin zabe ta kuma ba shi rashin nasara.

Daga bisani, ya garzaya zuwa Kotun Daukaka Kara inda a nan ma ta kori karar da ya ke neman tsige Gwamna Abiodun.

Kara karanta wannan

Bayan na Kano, Kotun Koli ta sake sanya ranar raba gardama a shari'ar neman tsige gwamnan Arewa

Har ila yau, ya kara daukaka kara zuwa Kotun Koli wanda a yanzu ta tanadi hukunci don sanin makomarsa nan da 'yan kwanaki.

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Alia

A wani labarin, Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue.

Hyacinth wanda dan jam'iyyar APC ne ya yi wa Ubangiji godiya kan wannan nasara da ya samu a Kotun Koli wacce ta kasance ta karshe.

Kotun ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Titus Uba wanda ke kalubalantar zaben Gwamna Alia.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.