NNPP Ta Fallasa Dabarar Karshe da APC Ta Kirkiro Kafin Yanke Hukuncin Shari’ar Kano
- Jam’iyyar NNPP ta zargi ‘yan APC da raba rigunan nasara a kotun koli tun kafin alkalai su yanke hukunci
- Hon. Abba Kawu Ali ya ce shugabannin APC a Kano sun fito da dabarar ne da nufin yaudarar al’umma
- Shugaban NNPP na kasar ya nemi ayi adalci a karar zaben da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya daukaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari ta fitar da jawabi na musamman a game da hukuncin shari’ar zaben jihar Kano.
Shugaban NNPP na rikon kwarya a kasa, Abba Kawu Ali ya fitar da sanarwar kamar yadda aka yada a wasu shafukan sada zumunta.
NNPP tayi magana a kan shari'ar Kano
Hadimin gwamna Abba Kabir Yusuf, Malam Salisu Hotoro ya wallafa sanarwar a Facebook, ba wannan ne karon farko daga NNPP ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam’iyyar NNPP ta kasa ta zargi APC mai adawa a Kano da neman yaudarar alkalan kotun koli a karar da Abba Kabir Yusuf ya daukaka.
NNPP ta ce 'yan APC sun kawo dabara
Jawabin Hon. Abba Kawu Ali ya ce ‘yan APC a jihar Kano su na raba huluna da rigunan da ke nuna alamar sun hango nasara a kotu.
Shugaban na NNPP yake cewa ana yin haka ne domin nuna tamkar za a tsige Abba Yusuf.
Tun da shari’ar zaben gwamnan jihar Kano tana gaban kotun koli, Kawu Ali ya ce bai dace wata jam’iyya ta nemi tursasa alkalai ba.
Abba v APC: Jawabin shugaban NNPP
"Shakka babu abin nan da APC ta ke yi kokarin tilastawa da barazana ne ga masu shari’a.
"Ra’ayin NNPP shi ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a matsayin na jagora a APC, ya ja-kunnen ‘yan jam’iyyarsa a Kano.
"Maganar gaskiya, rufewar idon ‘ya ‘yan APC a Kano ta kai intaha, idan ba ayi hattara ba, zai jefa jihar, Arewacin Najeriya da daukacin kasar nan cikin mummunan yanayi"
- Hon. Abba Kawu Ali
Jawabin ya kara da cewa ko makaho ya san NNPP ta doke jam’iyyar APC a zaben 2023 da aka yi a Kano, ta bukaci adalci a kotu.
Kiran Shekarau ga APC da NNPP
Kwanaki aka ji labari Ibrahim Shekarau ya fadawa Abba Kabir Yusuf, Nasiru Gawuna da mutanen Kano su roki zabi mafi alheri a kotu.
Malam Ibrahim Shekarau bai da wani zabi a shari’ar zaben gwamna da ke kotun koli.
Asali: Legit.ng