Shekarau Ya Fadi Na Zaba Tsakanin Abba Gida Gida da Gawuna Kafin Hukuncin Kotun Koli

Shekarau Ya Fadi Na Zaba Tsakanin Abba Gida Gida da Gawuna Kafin Hukuncin Kotun Koli

  • Fitaccen ‘dan siyasar nan, Ibrahim Shekarau ya maida lamarin shari’ar zaben gwamnan jihar Kano ga Allah SWT
  • Tsohon gwamnan ya yi kira ga masu neman mulki da mabiyansu su roki wanda zai fi zama alheri ga 'yan jihar Kano
  • Malam Shekaru ya tunawa NNPP da APC cewa Ubangiji SWT ne kurum yake bada mulki ga duk wanda Ya ga dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano -Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya tofa albarkacin bakinsa game da shari’ar zaben da ake yi a kotun koli.

A wata zantawa da aka yi da shi, Sanata Ibrahim Shekarau ya ba gwamna Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna shawara.

Kano.
Shari'ar Kano: Abba Kabir Yusuf da Nasiru Gawuna Hoto: Abba Kabir Yusuf da Dr Nasir Yusuf Gawuna
Asali: Facebook

Babban ‘dan siyasar ya yi kira ga gwamna mai-ci da Nasiru Yusuf Gawuna da kotu ta ce shi ya lashe zabe da su komawa Allah SWT.

Kara karanta wannan

Za mu shawo kan dukkan matsaloli tare da karfafa Najeriya - Ganduje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Shekarau ya bukaci ‘yan siyasar su roki zabin Ubangiji kuma su karbi duk kaddarar da ta auka masu bayan hukuncin kotu.

Malam Ibrahim Shekarau ya ce a roki alheri

Daily Trust ta fitar da labarin nan yanzu haka da ake jiran kotun koli ta yi hukunci karshe a shari’ar zaben gwamnan na jihar Kano.

Tsohon Ministan ilmin ya yi magana a Rumfar Afrika, ya ce abin da ya fi dacewa shi ne ayi addu’ar zabi mafi alheri ga mutanen Kano.

Shekarau wanda ya yi gwamna tsakanin 2003 da 2011 ya yi wannan addu’ar, sannan ya ce yana fatan APC da NNPP za tayi irin haka.

Babu laifi idan magoya baya da mabiya sun nuna zabinsu, amma a karshe tsohon gwamnan ya ce mafi alheri ake bukata ga Kano.

Shekarau bai marawa kowa baya ba

Kara karanta wannan

Shari'ar Zaben Kano: Ina da tabbacin samun nasara, Abba Kabir ya magantu, ya roki Kanawa

Duk wanda zai zama alheri ga Kanawa tsakanin Abba Gida Gida da Nasiru Gawuna, shi ne wanda Shekarau yake fatan ya yi nasara.

A wasu lokutan, tsohon gwamnan ya ce mutane suna tunani wanda Ubangiji Madaukaki ya ba mulki shi ne wanda Allah yake so.

Kano: ''Babu mai bada mulki sai Allah'' - Shekarau

A cewar Shekarau, Allah Madaukaki SWT yana bada mulki ne ga duk wanda ya ga dama, ya ce a tuna Ubangiji ne kadai Mai iko.

Yayin da shari’ar ta ke gaban Inyang Okoro, Shekarau ya ce Alkalai suna kokarin yin gaskiya ne bisa hujjojin da aka gabatar masu.

Shari'ar zaben Gwamnan Kano a kotun koli

Rahoton nan ya tabbatar da cewa nan da 'yan kwanaki za a san wanda ya yi nasara a shari'ar da ake yi a kan zaben jihar Kano na 2023.

Alkalai biyar su ka zauna a teburin kotun koli a karkashin jagorancin Inyang Okoro domin raba gardama a shari’ar zaben gwamnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng