Yanzun Nan: Babban Na Hannun Damar Obi Ya Yi Karin Haske Kan Yiwuwar Kafa Babbar Jam’iyya a Bidiyo
- Pat Utomi, ya ce akwai tattaunawa tsakanin yan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi da takwaransa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar
- Utomi ya bayyana cewa ya kuma tattauna da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- Manufar tattaunawarsa da manyan yan siyasar uku, ya ce, shi ne yadda za a kafa babbar jam’iyya gabanin zaben shugaban kasa na 2027
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Farfesa Pat Utomi, babban na hannun damar Peter Obi, ya bayyana cewa ya tattauna da mutuminsa, Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da sauran shugabannin jam'iyyun adawa kan shirye-shiryen kafa babbar jam'iyya.
Utomi ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a shirin Politics Today na Channels TV a daren ranar Laraba, 19 ga watan Janairu.
2027: Utomi na LP yana tunanin yin maja
Jaridar Legit ta rahoto cewa yayin da Obi da Utomi suka kasance jiga-jigan LP, Atiku da Kwankwaso suna rike da tutocin PDP da NNPP ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A tuna cewa shawarar da wasu jam'iyyun adawa suka yanke a 2013 na yin maja don zaben shugaban kasa na 2015 shine ya kawo karshen kudirin PDP na yin shekaru 60 a mulki.
Maja tsakanin rusasshiyar jam'iyyar NNPP, CPC, ACN, da wani bangare na APGA ne ya haifar da jam'iyyar APC mai mulki a yanzu.
Utomi yana tunanin maja domin yin waje da APC a babban zaben 2027.
Ya ce:
“Na yi magana da mafi yawa daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata game da wannan hanya da muke tafiya.
“Na tattauna da Alhaji Atiku Abubakar, na kuma tattauna da Injiniya Rabi’u Kwankwaso, na kuma tattauna da Peter Gregory Obi da mutane irin su Ralph Okey Nwosu na ADC da wasu daga cikin wadanda watakila su ne za su zama ginshiki.
“Na ce da su, ba magana a kanku ba ne, game da Najeriya ce, game da talakawan da ke titi ne, da gaske magana ce ta matsawa daga wannan sana’ar kashe mu raba ta hanyar siyar da mai zuwa yadda za mu zama daya daga cikin mafi kyawun tattalin arziki."
Kalli bidiyon Utomi a kasa:
Bwala ya ziyarci Tinubu a Villa
A wani labarin kuma, mun ji cewa Daniel Bwala, tsohon kakakin kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar, ya gana da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Bwala ya ce ya ziyarci fadar Villa ne "don nuna godiya da goyon bayan matakan da yake dauka wajen magance matsalolin da kasarmu me albarka ke fuskanta."
Asali: Legit.ng