“Sai Wata Rana PDP”: Na Hannun Damar Atiku Ya Gana da Tinubu a Villa, Hoto da Bidiyo Sun Bayyana
- Kakakin kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar a zaben 2023, Daniel Bwala, ya gana da Shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu
- Bwala, jigon PDP, ya gana da Shugaban Tinubu a fadar Villa da ke babban birnin tarayya Abuja
- Da yake jawabi a shafinsa na X, Bwala ya ce ya ziyarci fadar Shugaban kasar ne don goyon bayan salon shugabancin Tinubu
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Fadar shugaban kasa, Abuja - Daniel Bwala, tsohon kakakin kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar, ya gana da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Bwala ya ce ya ziyarci fadar Villa ne "don nuna godiya da goyon bayan matakan da yake dauka wajen magance matsalolin da kasarmu me albarka ke fuskanta."
Bwala Daniel ya gana da Tinubu
Jaridar Legit ta rahoto cewa Bwala ya kasance mai goyon bayan Tinubu kuma dan jam'iyyar APC mai mulki kafin ya koma PDP a lokacin zaben 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon na PDP ya yada hotonsa yayin da suke musabaha da shugaban kasar. Ya kuma saka hoton bidiyo na dakika 13 na ziyarar da ya kai wa shugaban Najeriyan.
Ziyarar da ya kai wa shugaban kasar a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu, ta haifar da martani daban-daban a shafukan sada zumunta, inda wasu masu amfani da soshiyal midiya suka rasa inda (Bwala) ya dosa.
Martanin yan Najeriya kan ziyarar
@RealQueenBee_ ya ce:
"Ma'aikatan siyasa sun karade ko'ina a Najeriya."
@emmanuel_yours ya yi martani:
"Sai wata rana PDP. Babu wanda ke son "kasa mai inganci", kowa kansa yake so wa abu."
@abdullahayofel ya rubuta:
"Daniel Bwala ka kasa zama da yunwa na shekara daya kacal. Lmao."
Atiku ya yaba ma Tinubu
A wani labarin, mun ji cewa Atiku Abubakar yana ganin Bola Ahmed Tinubu ya cancanci yabo a dalilin daukar mataki a kan Betta Edu da aka yi.
Jagoran adawar ya fitar da jawabi ta ofishin Phrank Shaibu a game da dakatar da Ministar jin-kai ta Najeriya, Dr. Betta Edu.
Mai taimakawa ‘dan takaran shugaban kasan a PDP wajen hulda da jama’a, ya ce an yi daidai da aka dauki matakin da ya dace.
Asali: Legit.ng