Mataimakin Gwamna Ya Bayyana Irin Cin Amanar da Gwamnan PDP Ya Yi Masa, Ya Sha Sabon Alwashi
- Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya koka kan abin da ya kira cin amanarsa da Gwamna Godwin Obaseki ya yi
- Shaibu ya yi nuni da cewa gwamnan ya ci amanarsa ta hanyar ƙin goyon bayan burinsa na zama gwamnan jihar
- Sai dai, duk da zafin cin amanar da gwamnan ya yi masa, Shaibu ya ce za su bijire masa kan yunƙurin kawo bare da yake yi domin ya zama gwamnan jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya bayyana cin amanar da Gwamna Godwin Obaseki, ya yi masa kan rashin marawa takararsa baya a zaɓen gwamna mai zuwa na 2024.
Shaibu, wanda ya yi ikirarin cewa lallaɓa shi aka yi ya zama mataimakin gwamna na Obaseki, ya ce ya ƙara wa gwamnatin Obaseki ƙima ta fuskar tsarin siyasa da kuma kuɗaɗensa.
Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa da yake magana a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a safiyar Laraba, Shaibu ya ce ya ji zafi sosai saboda Obaseki yana goyon bayan wani bare maimakon shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shaibu ya koka da cewa duk da goyon bayansa da kuma ƙara wa Obaseki ƙimar siyasa, ya ci amanar sa, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Wane irin cin amana Obaseki ya yi wa Shaibu?
A kalamansa:
"Kujerar gwamnan jihar Edo ba za ta so bare ba, kuma gwamnan yana ƙoƙarin kawo wani bare, za mu bijire masa. Ina yin wannan takarar ne ba domin burga ba, sai domin mutane suna ra'ayi na.
“Duk inda na je, kuna iya ganin ƙaunar da ake nuna min, goyon bayan da ake nuna min ba shiri bane kamar yadda gwamna ke amfani da kuɗin al'ummar jiha wajen neman goyon baya ga ɗan takarar sa.
"Na ji zafin cin amanar da gwamnan ya yi min. Na bada gudunmawa ta fuskar ƙimar siyasa, kuɗi da tsarin siyasa domin wa'adi na biyu na Gwamna Obaseki.
Obaseki da Shaibu dai sun fara takun-saƙa ne tun bayan fara wa’adi na biyu na gwamnan.
A yayin da ake ta cece-kuce, Shaibu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a jihar.
Shaibu Ya Koka Kan Rashin Biyansa Albashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya koka kan yadda Gwamna Obaseki ya riƙe masa haƙƙoƙinsa.
Shaibu ya yi nuni da cewa ya shafe watanni shida kuɗi ba su shigo ofishinsa ba saboda takun saƙar da yake yi da gwamnan.
Asali: Legit.ng