Gbajabiamila ya Fadi Wadanda Suka Taimaki Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa

Gbajabiamila ya Fadi Wadanda Suka Taimaki Bola Tinubu Ya Zama Shugaban Kasa

  • Femi Gbajabiamila ya ce ba za a raba nasarar Bola Ahmed Tinubu a siyasa da tsofaffin abokansa a majalisa ba
  • Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriyan ya yi wannan bayani da wata kungiyarsu ta yi taro a garin Abuja
  • Abokan Femi Gbajabiamila a majalisa sun kira liyafa inda hadimin shugaban kasar ya bada gudumuwar N50m

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya alakanta nasarar Bola Ahmed Tinubu da mutanensa a siyasa.

Daily Trust ta rahoto Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya na cewa dangantakar da Bola Ahmed Tinubu ya kulla da yake Sanata ne ya cece shi.

Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Aminan Femi Gbajabiamila sun yi taro

Tsohon shugaban majalisar wakilan ya bayyana haka ne a wajen wata liyafar da tsofaffin ‘yan majalisar tarayya su ka shirya masu a Abuja.

Kara karanta wannan

"Burin kowane ɗan Najeriya ya ɗauki hoto da ni" Ministan Tinubu ya yi magana mai jan hankali

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda su ka shirya wannan taro sun zama ministoci, sanatoci, ko gwamnonin jihohi a yau.

A cikin tsofaffin abokan aikin babban hadimin shugaban Najeriyan akwai gwamna Umar Bago da Ministan wasanni, Hon. John Enoh.

Femi Gbajabiamila ya godewa abokansa da su ka shirya taron, ya nuna takaicinsa ganin yadda wasu ba su samu damar halarta ba.

Femi Gbajabiamila a kan Bola Tinubu

"Bari in fada maku wani abu guda a yau, ba dole Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sani ba, na dade tare da shi,
Kuma daga cikin manyan karfinsa wadanda suka kai shi matsayin da yake a yau shi ne tsofaffin abokan aikinsa a lokacin ya na Sanata.
Saboda haka wannan majalisa ce da kamata mu rike da muhimmanci. Bai kamata mu jefar da kujera bayan mun dare kai ba."

- Femi Gbajabiamila

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi martani yayin da Tinubu ya dakatar da Betta Edu, ya yi shagube ga Buhari

An karrama abokan Femi Gbajabiamila

Leadership ta rahoto cewa ‘dan majalisar ya ba majalisarsa ta su gudumuwar N50m.

Sanata Osita Izunaso wanda yana cikin kungiyar, ya yi kira da a rika tafiya da tsofaffin ‘yan majalisa a sha’anin gwamnati da jam’iyya.

Ibrahim Zailani wanda shi ne shugaban kungiyar ya bada lambar yabo ga John Enoh.

Bola Tinubu yana binciken zargin sata

A wani rahoton na dabam, an ji cewa zargin Ministocin da aka nada domin yakar talauci da satar miliyoyin kudin talakawan kasa.

Yanzu haka EFCC ta na binciken Dr. Betta Edu da Hajiya Sadiyar Umar Farouk wanda ta gabace ta, kuma an karbewa dukkansu fasfo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel