Jerin Sunayen Ministoci 6 da Aka Sallama Kan Zargin Badakalar Kudade Tun 1999
Tun bayan dawo wa mulkin dimukradiyya a shekarar 1999 an samu kitumurmura da matsaloli tattare da wasu masu rike da mukamai.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
An samu wasu matsaloli da ya haddasa korar masu ministoci a gwamnatoci da dama yayin da wasu suka yi murabus a mukamansu.
Tun daga Olusegun Obasanjo har zuwa Shugaba Tinubu an samu sauye-sauye a mukamai ko kuma korar wasu daga cikinsu saboda wasu matsaloli.
Mafi yawansu an zarge su da badakalar kudade yayin da wasu suka shiga tsautsayin sauyin gwamnati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta tattaro muku jerin ministocin da aka kora a mukaminsu da kuma dalilin korar:
1. Barth Nnaji
Yayin da fadar shugaban kasa a wancan lokaci ta ce ya yi murabus a karan kansa, ta tabbata an tilasta Nnaji ne saboda wasu badalakar kwangila.
Tsohon shugaban kasar, Goodluck Jonathan ya ce ya nemi Nnaji ya yi murabus madadin ya kore shi, cewar The Nation.
2. Michael Aondoakaa
An nada Aondoakaa a matsayin Atoni-Janar a gwamnatin marigayi Umaru Yar’adua a shekarar 2007.
A shekarar 2010, Jonathan ya sallame shi cikin wani irin yanayi bayan ya zama shugaban kasa na riko bayan rasuwar Yar’adua.
3. Fabian Osuji
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya sallami Osuji bayan EFCC ta zarge shi da badakalar miliyan 55 a kasafin kudin Majalisar Tarayya, The Capital ta tattaro.
4. Stella Oduah
Goodluck Jonathan ya sallami Oduah daga mukamin Ministar harkokin jiragen sama kan badakalar kudade.
Daga bisani hukumar EFCC ta ci gaba da binciken Oduah a shekarar 2020 da wasu mutane takwas.
5. Farfesa Adenike Grange
Tsohuwar Ministar kiwon lafiya ta yi murabus bayan matsin lamba ta samu a mulkin Umaru Yar’adua kan badakalar miliyan 300.
Ta tabbatar da cewa ta gamu da shawarwari marasa kyau ne daga daraktocin ma’aikatar.
6. Betta Edu
Shugaba Tinubu ya dakatar Edu kan zargin kokarin badakalar naira miliyan 585, cewar Premium Times.
Edu wacce it ace Ministar jin kai da walwala ta sha suka bayan zargin da ake mata ya fito fili.
An dakatar da Edu daga mukamin Minista
A wani labarin, Shugaba Tinubu ya dakatar da Ministar jin kai da walwala, Betta Edu daga mukaminta.
Ana zargin Edu da badakalar miliyan 585 inda ta yi kokarin tura wa wani asusun banki na daban.
Asali: Legit.ng